Sinopsis

Masu Saurare na aiko da Tambayoyinsu domin neman amsa a shirin, Ana gabatar da shirin ne a karshen mako.

Episodios

 • Darajar kudin Bitcoin

  Darajar kudin Bitcoin

  06/01/2018 Duración: 19min

  A cikin shirin  za mu kawo maku wasu daga cikin amsoshin da suka shafi  tattalin arziki kama daga Bitcoin. Akwai wasu tambayoyin da muka mika zuwa  mutanen da suka dace.

 • Tarihin jihar Kaduna dake tarrayar Najeriya

  Tarihin jihar Kaduna dake tarrayar Najeriya

  30/12/2017 Duración: 19min

  A cikin shirin amshoshin masu saurare Azima Aminu ta jiyo ta bakin masana tarihi kan kafuwar Jihar Kaduna . Ta kuma samo wasu daga cikin amsoshin masu saurare rfi a cikin shirin.

 • Tarihin akwatin rediyo

  Tarihin akwatin rediyo

  09/12/2017 Duración: 19min

  A cikin shirin amsoshin masu saurare,Azima Aminu ta yi kokarin samo amsar tambayar tarihin akwatin Rediyo da wasu tambayoyin can daban.   sai ku biyo mu.....

 • Tarihi da karin haske kan yanayin siyasar kasar Iran

  Tarihi da karin haske kan yanayin siyasar kasar Iran

  02/12/2017 Duración: 20min

  Shirin Tambaya da Amsa na wannan makon ya yi karin haske ne kan Tarihi da kuma salon siyasar kasar Iran. Zalika shirin ya amsa tambayar masu sauraro kan tarihin tsohon shahararren dan wasan kwallon kafa na kasar Liberia kuma dan takarar shugabancin kasar wato George Weah.

 • Karin bayani kan asali ko tushen harshe

  Karin bayani kan asali ko tushen harshe

  25/11/2017 Duración: 19min

  Shirin na wannan mako ya yi karin haske kan tambayoyin da masu sauraro suka nemi karin haske a kai, daga ciki akwai karin bayani kan asali ko kuma tushen harshe, sai kuma neman sanin amfanin wakan jego ga macen da ta haihu.

 • Tarihin Kungiyar Al Shebab

  Tarihin Kungiyar Al Shebab

  04/11/2017 Duración: 19min

  Kungiyar Al Shebab na Somalia  na daya daga cikin kungiyoyin dake  barazana ga batun tsaroa  akasar Somalai   da wasu kasashen ketare. A cikin shirin amsoshin masu saurare Azima Aminu  Bashir ta duba tambayar wani mai sauraren mu ,ga kuma shirin amsoshin tambayoyin ku masu saurare.

 • Tarihin kungiyar al Shebaab da dalilan da ya sa suka addabi Somalia

  Tarihin kungiyar al Shebaab da dalilan da ya sa suka addabi Somalia

  28/10/2017 Duración: 19min

  Shirin Tambaya da Amsa na wannan yayi karin haske kan bukatar samun tarihin Kungiyar Al Shebaab mai da'awar Jihadi a kasar Somalia, da kuma dalilian da suka sanya har yanzu aka kasa kawo karshensu. Zalika shirin na dauke da amsoshin wasu tambayoyin da masu sauraro suka turo.

 • Tarihin Kaigaman Adamawa, Farfesa Pate

  Tarihin Kaigaman Adamawa, Farfesa Pate

  14/10/2017 Duración: 20min

  Shirin tambayoyi da amsa na wannan makon ya yi kokarin amsa tambayoyi da daban daban da muka samu daga masu saurarenmu, in da muka fara da tambayar da ke bukatar tarihin Kaigaman Adama, Farfesa Umar Pate. Kazalika shirin ya ci gaba da hira da gogeggen dan siyasar Nijar, wato Dr. Sanusi Tambari Jako.

 • Ci gaban tarihin Sanusi Tambari Jaku na Nijar

  Ci gaban tarihin Sanusi Tambari Jaku na Nijar

  07/10/2017 Duración: 19min

  Shirin tambayoyi da amsa na wannan makon tare da Garba Aliyu Zaria ya amsa tambayoyin da masu saurare suka aiko, ciki har da tambayar da ta bukaci tarihin tsohon dan siyasa a Nijar, Dr. Sanusi Tambari Jaku.

 • Tarihin Dokta Sanoussi Jackou daga Jamhuriyar Nijar

  Tarihin Dokta Sanoussi Jackou daga Jamhuriyar Nijar

  30/09/2017 Duración: 20h00s

  A cikin shirin tambaya da amsa daga sashen hausa na rediyon Faransa RFI,masu saurare sun bukaci Garba Aliyu ya  kawo masu tarihin dan siyasar Nijar Dokta Sanoussi Tambari Jackou.  

 • Tarihin Tsibiri a ckin shirin amshoshin tambayoyin masu saurare

  Tarihin Tsibiri a ckin shirin amshoshin tambayoyin masu saurare

  23/09/2017 Duración: 19min

  A cikin shirin tambayoyin ku masu sauraren sashen hausa na gidan rediyon Faransa Rfi ,za ku ji ko a ina aka kwana dangane da batun  masarautar Tsibiri dake Jamhuriyar Nijar dama wasu amsoshin tambayoyin ku a kai.      

 • Karin bayani kan alakar sauyin yanayi da kuma guguwa da ke tasowa daga teku

  Karin bayani kan alakar sauyin yanayi da kuma guguwa da ke tasowa daga teku

  17/09/2017 Duración: 20min

  Daya daga cikin batutuwan da shirin Tambayoyinku da Amsa na wannan makon yayi karin haske a kai shi ne; Alakar canjin yanayi da aukuwar guguwa, kashe-kashenta da kuma yadda guguwar ke tasowa daga teku.

 • Tarihin masarautar Kanem Borno da alakarta da sauran masarautu

  Tarihin masarautar Kanem Borno da alakarta da sauran masarautu

  03/09/2017 Duración: 17min

  Shirin Tambaya da Amsa wanda a makonnan Salisou Hamisou ya gabatar, ya amsa tambayar da ku masu sauraro kuka gabatar, ta neman karin bayani kan masarautar Kanem Borno da kuma alakarta da sauran masarautun waccan lokacin da ke ciki da wajen Najeriya. Sai kuma sauran tambayoyin da shirin ya amsa kan wasu fannonin daban.

 • Shiek Abdullahi Uwais: Karin haske kan alamuran da suka shafi Layya

  Shiek Abdullahi Uwais: Karin haske kan al'amuran da suka shafi Layya

  26/08/2017 Duración: 20min

  Shirin Tambaya da Amsa na wannan mako da AbduRahman Gambo Ahmad ya gabatar, ya yi karin haske ne kan tambayoyin da masu sauraro suka aiko kan neman karin bayani bisa al'amuran da suka shafi Ibadar Layya, Lafiya (bayani kan ciwon Basir), sai kuma rikicin yankin gabas ta tsakiya.

 • Hanyoyin warkar da cutar kuturta

  Hanyoyin warkar da cutar kuturta

  19/08/2017 Duración: 20min

  A cikin shirin  amsoshin tambayoyin masu saurare,mu ji ta bakin likita  dangane da cutar kuturta dama hanyoyin warkar da ita.    

 • Amfanin cin namijin Goro

  Amfanin cin namijin Goro

  12/08/2017 Duración: 19min

  A cikin shirin tambaya da amsa ,Abdurahamane Gambo ya samu zantawa da masana dangane da wasu daga cikin tambayoyin ku,kamar wannan tambaya ko mai nene amfanin cin namijin goro,ga dai amsar a cikin shirin amsoshin ku masu saurare.  

 • Tarihin Shahararren Magini Na Kasar Hausa Muhammadu Durugu wanda aka fi sani da Babban Gwani

  Tarihin Shahararren Magini Na Kasar Hausa Muhammadu Durugu wanda aka fi sani da Babban Gwani

  05/08/2017 Duración: 20min

  Cikin wannan shiri za'a ji tarihin wani shahararren magini Muhammadu Durugu wanda aka fi sani da Babban Gwani a kasar Hausa. Akwai kuma amsar tambaya game da gandun daji na Bauchi dake Arewacin Najeriya.

 • Kamfanin dilancin labaran Faransa na Afp ,mai nene sahihancin kamfanin

  Kamfanin dilancin labaran Faransa na Afp ,mai nene sahihancin kamfanin

  15/07/2017 Duración: 19min

  Kamfanin dilancin labaran Faransa na AFP ya fara aiki  a shekara ta 1944, cibiyar kamfanin na Paris a kasar Faransa. a ckin shirin amshoshin masu saurare za ku ji karin haske  a kai.    

 • Rayuwar Marigayi Dan Masanin Kano Yusuf Maitama Sule

  Rayuwar Marigayi Dan Masanin Kano Yusuf Maitama Sule

  08/07/2017 Duración: 19min

  Shirin ya amsa tambayoyin da masu saurare suka aiko inda suka nemi bayani akan rayuwar Marigayi Alhaji Yusuf Maitama Sule Dan Masanin Kano da Allah Ya yi wa rasuwa. Shirin ya tattauna da abokinsa kuma amininsa Galadiman Katsina Mai tsohon Alkalin Alkalan Najeriya mai Shari'a Mamman Nasir. Sannan akwai tambaya akan asalin Aula Sarkin dubara.

 • Bambancin Turancin Ingila da na Amurka

  Bambancin Turancin Ingila da na Amurka

  01/07/2017 Duración: 20h00s

  Shirin ya yi kokarin amsa tambayoyi da suka shafi banbancin da ke tsakanin Turancin Ingila da na Amurka da kuma tambaya akan lafiyar dabbobi, ta yadda cuta ke yaduwa a tsakaninsu.

página 5 de 5