Tambaya Da Amsa

Informações:

Sinopsis

Masu Saurare na aiko da Tambayoyinsu domin neman amsa a shirin, Ana gabatar da shirin ne a karshen mako.

Episodios

  • Sanadin katsewar kafofin sadarwa na Internet a nahiyar Afirka

    23/03/2024 Duración: 20min

    shirin a wannnan mako zai ba da hankali ne akan abinda ya kai ga katsewar hanyoyin sadarwa na internet a wasu sassa na Nahiyar Afirka.

  • Karin bayani a kan ‘yan sandan kasa da kasa na Interpol

    16/03/2024 Duración: 20min

    Shirin yana zuwa muku ne da amsoshin tambayoyin da masu sauraronmu suka aiko mana, kuma duk mako yake zuwa mukua wannan tasha kuma a daidai wannan lokaci. Daga cikin tambayoyin da za mu amsa a yau, za mu ji karin bayani a kan ‘yan sandan kasa da kasa na Interpol. Abokinku, Michael Kuduson ne ke muku lale marhabun.

  • Neman bayanni a game da mayar da kasa saniyar ware

    09/03/2024 Duración: 20min

    Kamar yadda muka saba, shirin yana zuwa muku ne da amsoshin tambayoyin da masu sauronmu suka aiko mana, kuma duk mako yake zuwa muku a wannan tasha kuma a daidai wannan lokaci. Daga cikin tambayoyin da za mu amsa a yau, akwai wadda ke neman bayanni a game da mayar da kasa saniyar ware, da kuma tasirin haka a kan kasar da aka maida saniyar ware.

  • Amsoshin wasu daga cikin tambayoyin masu saurare daga Rfi

    02/03/2024 Duración: 20min

    A cikin shirin na wannan mako,Michael Kuduson ya duba wasu daga cikin tambayoyin,ko wadanan hanyoyi ne ake bi domin samun tikiti kujerar wakili a Kwamity tsaro na MDD.Ya kuma duba wasu tambayoyi da suka jibanci bangaren tsaro da sauren su.

  • Tarihin yan tawayen Houthi na Yemen

    17/02/2024 Duración: 20min

    A cikin shirin tambaya da amsa na wannan mako, Michael Kuduson ya mayar da hankali a tambayar da ta shafi yan Tawayen Houthi na kasar Yemen.Sai ku biyo mu.

  • Tambaya da Amsa: Cikakken tarihin Hausawa 'yan asalin kasar Mali

    10/02/2024 Duración: 20min

    Daga cikin tambayoyin da za mu amsa a yau, akwai wadda ke neman sanin tarihin Hausawa ‘yan asalin kasar Mali.  Danna alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Micheal Kuduson.

  • Ko me ya sa gwamnonin jihohi a Najeriya ba su da iko a kan jami’an tsaro?

    03/02/2024 Duración: 20min

    Shirin ‘Tambaya Da Amsa’ yana kawo muku amsoshin tambayoyin da masu sauraronmu suka aiko mana ne, kuma duk mako yake zuwa muku a daidai wanna lokaci, kuma a wannan tasha. Ko me ya sa gwamnonin jihohi a Najeriya ba su da iko a kan jami’an tsaro? Wannan tambayar na daya daga cikin tambayoyin da za mu amsa a yau. Sai ku kasance tare da abokinku, Michael Kuduson.

  • Neman karin bayani a kan Somaliland da ko kasa ce mai ‘yanci?

    27/01/2024 Duración: 20min

    Shirin ‘Tambaya Da Amsa’ yana zuwa muku ne da amsoshin wasu daga cikin tambayoyin da wsu daga cikin masu sauraronmu suka aiko mana, kuma duk mako ya ke zuwa muku a daidai wannan lokaci.Daga cikin tambayoyin da za mu amsa a yau, akwai wadda ke neman karin bayani a kan Somaliland da ko kasa ce mai ‘yanci. Sai a biyo

  • Bayani a kan ramukan sararin samaniya (Black Holes)

    20/01/2024 Duración: 19min

    Kamar yadda aka saba, shirin yana kawo muku amsoshin tambayoyin da wasu daga cikin masu sauraronmu suka aiko  mana ne, kuma duk mako  yake zuwa muu a daidai wannan lokaci. Daga cikin tambayoyin da za mu amsa, akwai wadda ke neman bayani a kan ramukan nan da ke sarari, wadanda ake kira ‘black holes. 

  • Dalilan da suka hana kasashe masu tasowa dogaro da kansu a bangaren tsaro

    16/12/2023 Duración: 19min

    Shirin ‘Tambaya Da Amsa ‘ yana zuwa muku ne kowane mako a wannan tasha, inda ya  ke kawo amsoshin tambayoyin da suka samu shiga daga masu sauraronmu. Daga cikin tambayoyi da za mu amsa a yau, akwai wadda ke neman bayani a kan dalilin da ya sa kasashe masu tasowa ba iya dogaro da kan su wajen yaki da matsalar tsaro,, musamman ma ta’addanci da sauransu.

  • Bayani a kan masu 'kujerar naki' a Majallisar Dinkin Duniya

    18/11/2023 Duración: 20min

    Shirin 'Tambaya Da  Amsa' na wannan mako kaamar kowane mako, ya kawo muku tambayoyi ne da masu sauronmu suka aiko  mana, inda  ya samar da amsoshinsu daidai gwargwadon iko. Daga cikin tambayoyin da muka amsa a yau, akwai wadda ke neman sanin yadda aka yi wasu kebabbun kasashe suka samu "kujerar naki' a Kwamitin Tsaro nna Majalisar Dinkin Duniya.

  • Tambaya dangane da bayani a kan kisan kare dangin Holocaust

    11/11/2023 Duración: 20min

    Tambaya daga Alhaji Haruna Kira da  Umar Ladan Baturiya daga jihar Jigawa Najeriya. So suke a banbanta  musu tsakanin ta’addanci da ayyukan ‘yan bindiga. Ko akwai dokar da ke hana amfani da karfi fiye da kima a kan irin wadannan masu aikata manyan laifuka?

  • Amsoshin tambayoyin da wasu daga cikin masu sauraron RFI

    04/11/2023 Duración: 20min

    Me ake nufi da karbar rance na biliyoyin daloli don tallafa wa naira kamar yadda gwamnatin Najeriya ta yanzu ta  yi. Mataki ne mai fa’ida? Shirin ‘Tambaya Da Amsa’ ne ke zuwa ma mai sauraro daga sashen Hausa na Radio France Internationale RFI. Ana iya aiko da tambayar da ake da ita ta adireshinmu na imel a rfihausatambayoyi@gmail.com .

  • Bayani a kan ramin mafi tsawo a duniya, wadda ke gabashin nahiyar Afrika

    28/10/2023 Duración: 20min

     ‘Tambaya Da Amsa’, daga sashen Hausa na Radio France Internationale, RFI,  tare da abokin nan naku, Michael Kuduson.Shiri ne da ke kawo muku amsoshin tambayoyin da wasu daga cikin masu sauraronmu suka aiko mana, duk mako yake  zuwa daga wannan tasha, kuma a lokaci irin wannan. Daga cikin tambayoyn da za mu amsa a yau, akwai wadda ke neman bayani a kan ramin nan mafi tsawo a duniya, wadda ke gabashin nahiyar Afrika, wato East  African Rift.

  • Karin bayani a kan Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya

    21/10/2023 Duración: 20min

    Shirin yana zuwa muku ne da wasu daga cikin tambayoyin da  masu sauraronmu suka aiko mana, kuma duk mako yake zuwa muku a wannan tasha, kuma a daidai wannan lokaci. A cikin Shirin wannan makon, zai amsar tambayar da ke neman Karin bayani a Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da kuma gazawarsa da ma majalisar wajen kawar da yake yake a duniya,

  • Dalilan da suka haddasa barkewar yaki tsakanin Isra'ila da mayakan Hamas

    14/10/2023 Duración: 20min

    Shirin 'Tambaya da Amsa' na wannan makon tare da Micael Kuduson, mayar da hankali kan neman karin bayani dangane da musabbabin sake barkewar rikici tsakanin kungiyar Hamas ta yankin Falasdinu da Isra’ila. Akwai kuma wasu karin tambayoyin da shirin ya yi wa masu sauraro karin bayani akai.

  • Shirin Tambaya da Amsa na wannan mako ya tabo batun cutar dake maida mutum zabaya

    30/09/2023 Duración: 20min

    kamar yadda aka saba a ko wane mako shirin Tambaya da Amsa tare da Michael KJuduson,  na mayar da hankali wajen amsa muhimman tambayoyin da kuka buka ci fita daga jahilcinsu. ina a wannan  mako, shirin  ya tabo batutuwa da dama, da suka hada da  son sanin irin cutar dake  kone fatar bakaken fata ta na zama farar sal.

  • Tambaya da Amsa: Amsar tambaya kan alakar girgizar kasa da aman wutar dutse

    23/09/2023 Duración: 20min

    Shirin Tambaya da Amsa tare da Michael Kuduson a wannan mako ya amsa tambayoyin da masu saurare suka aiko, kuma a wannan makon za ku ji ci gaban amsa kan dalilan da ke haddasa girgizar kasa dama dangantaka tsakanin wannan matsala da aman wutar dutse da kasashe da dama ke fama da su. Haka zalika akwai amsa game da tarihin Marigayi Malam Amadou mai wa'azi na jihar Damagaram a Jamhuriyyar Nijar wanda ya koma ga mahaliccinsa a ranar 3 ga watan Satumbar da muke ciki ya na da shekaru 73 a Duniya.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin...........

  • Fashin baki kan abin da ke haddasa girgizar kasa a duniya

    16/09/2023 Duración: 20min

    Kamar yadda muka saba a duk mako, shirin yana zuwa  muku ne da amsoshin wasu daga cikin tambayoyin da masu sauraronmu suka aiko mana kan duk wani abin da ya shige musu duhu.

  • Fashin baki kan yawan juyin mulki a Yammacin Afirka

    09/09/2023 Duración: 19min

    Kamar yadda muka saba a duk mako, shirin yana zuwa  muku ne da amsoshin wasu daga cikin tambayoyin da masu sauraronmu suka aiko mana kan duk wani abin da ya shige musu duhu. Daga cikin tambayoyin da za mu amsa a yau, akwai wadda ke neman fashin baki a kan yadda juye-juyen mulki suka yi wa yankunan Yammaci da Gabashin Afrika dabaibayi a baya bayan nan.

página 1 de 2