Bakonmu A Yau

Arewa maso Yammacin Najeriya ne mafi hatsari saboda matsalar tsaro - Bincike

Informações:

Sinopsis

Kungiyar 'Global Rights' ta bayyana yankin arewa maso yammacin Najeriya a matsayin mafi hadari, saboda yadda 'yan bindiga ke kisa da take hakkin Bil Adama ba tare da kaukautawa ba. Kungiyar tace a cikin shekaru 10 da suka gabata, yankin ya gamu da mummanar ukuba, fiye da sauran sassan Najeriya.Bashir Ibrahim Idris ya tintibi Dr Murtala Ahmad Rufai na Jami'ar Usman Danfodio, mawallafin 'I am a Bandit' kuma mai bincike a kan matsalar tsaron yankin.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.