Bakonmu A Yau

Yadda rayuwa ta kasance bayan da muka faɗa hannun mayakan Boko Haram - Maryama

Informações:

Sinopsis

A ranar Lahadi, 14 ga watan Afrilun nan aka cika shekaru 10 da sace dalibai mata na makarantar sakandaren Chibok sama da 250 da mayakan Boko Haram suka yi a jihar Borno. Bayan shafe wannan tsawon lokkaci dai har ya zuwa yau ba a iya gano wasu daga cikinsu ba.Ɗaya daga cikin daliban da suka kuɓuta mai suna Maryama, ta shaidawa Bashir Ibrahim Idris irin abubuwan da suka faru, daga lokacin da aka sace su da kuma lokacin da ta kuɓuta bayan shekaru 3.