Bakonmu A Yau

Tattaunawa da Bashir Ɗan Malam kan tsadar farashin mai a arewacin Najeriya

Informações:

Sinopsis

Harkokin kasuwanci da dama sun durkushe musamman a yankin arewacin Najeriya sakamakon tsadar farashin man fetur, inda ake sayar da lita guda a kan naira 2,000 zuwa 2,500  a kasuwar bayan-fage a jihar Sokoto. Kodayake akwai sassaucin farashin man a yankin kudancin kasar.  Wannan kuwa na zuwa ne bayan watanni 11 da gwamnatin tarayya ta janye tallafin man fetur da zummar bai wa kasuwa damar yin halinta. Kan haka Abdurrahman Gambo Ahmad ya tattauna da Alhaji Bashir Dan Malam,shugaban Ƙungiyar Dillalan Man fetur da Iskar Gas na Kasa a Najeriya.Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar hirar