Bakonmu A Yau

Sanata Umar Ibrahim Tsauri kan matsayar gwamnonin PDP halin da Najeriya ke ciki

Informações:

Sinopsis

A ƙarshen makon da ya gabata ne gwamnonin PDP suka gudanar da taronsu a jihar Filato, wanda ya tattauna halin da Najeriya ke ciki da kuma makomar jam'iyyarsu. Bayan kammala taron gwamnonin sun buƙaci shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu da ya sake nazari kan manufofinsa na tattalin arziki saboda illar da yake yiwa talakawa. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da tsohon Sakataren Jam'iyyar PDP na ƙasa, Sanata Umar Ibrahim Tsauri. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar zantawarsu..........