Bakonmu A Yau

Tattaunawa da Muhammad Dahiru Dan Adam kan ƙalubalen naƙasassu a jihar Lagos

Informações:

Sinopsis

Yau ce ranar da Majalisar ɗinkin duniya ta ware domin tunawa da halin da masu buƙata ta musamman ke ciki da kuma duba hanyoyin da za a inganta rayuwarsu. Karibullahi Abdulhamid Namadobi ya yi tattaki zuwa wani gida a jihar Lagos mai ɗauke da irin waɗannan mutanen sama da dubu 3 da suka fito daga yankunan arewacin Najeriya. Ga yadda zantawarsa ta gudana da guda cikin shugabanninsu Muhammad Dahiru Dan Adam.