Sinopsis

Masu Saurare na aiko da Tambayoyinsu domin neman amsa a shirin, Ana gabatar da shirin ne a karshen mako.

Episodios

 • Tambaya da Amsa - Shirin Tambaya da Amsa tare da Micheal Kuduson 20-07-2019

  Tambaya da Amsa - Shirin Tambaya da Amsa tare da Micheal Kuduson 20-07-2019

  20/07/2019 Duración: 20min

  Shirin Tambaya da amsa tare da Micheal kuduson ya amsa muhimman tambayoyi tare da tuntubar masana daga fannoni daban-daban,ciki kuwa har da matakan da aka bi wajen damkawa Jamhuriyar Kamaru yankin Bakassi. ayi saurare lafiya.

 • Tambaya da Amsa - Aikin lauya a Najeriya ,da kuma hanyoyin samu lambar girma ta SAN

  Tambaya da Amsa - Aikin lauya a Najeriya ,da kuma hanyoyin samu lambar girma ta SAN

  13/07/2019 Duración: 19min

  Mahmud Salihu Kaura Namoda, jihar Zamfara a tarayyar Najeriya, so yake a mai bayanin yadda lauya a Najeriya ke iya zama babban lauyan kasa mai lambar girmamawa ta SAN. Mickael Kuduson ya duba wasu daga cikin tambayoyin masu saurare.

 • Tambaya da Amsa - Tsarin yadda za a rika amfani da kudin bai-daya na kasashen ECOWAS

  Tambaya da Amsa - Tsarin yadda za a rika amfani da kudin bai-daya na kasashen ECOWAS

  06/07/2019 Duración: 19min

  Shirin Tambaya da Amsa na wannan makon ya tuntubi masana dangane da wasu daga cikin batutuwan da masu sauraro suka nemi karin bayani akai, da suka hada da bayani kan tsarin yadda za a rika amfani da kudin bai-daya na kasashen ECOWAS, sai kuma dalilan rikicin Amurka da Iran, da kuma kasashen da rikicin zai shafa.

 • Tambaya da Amsa - Dalilan da ke sanya kai harin Intanet dama wadanda suka fara kai harin a tarihi

  Tambaya da Amsa - Dalilan da ke sanya kai harin Intanet dama wadanda suka fara kai harin a tarihi

  29/06/2019 Duración: 26min

  A cikin shirin Tambaya da Amsa tare da Micheal Kuduson na wannan mako za su amshi tambayoyin da suka hada da dalilan da kan sanya kakabawa kasa takunkumi, tarihi fara kai harin Intanet da ma kasar da ta fara kai shi, da dai sauran amsoshin tambayoyin da ku masu saurare kuka aiko man. Asha saurare Lafiya.

 • Tambaya da Amsa - Kasar dake da karfin tattalin arziki a Duniya dama Afrika

  Tambaya da Amsa - Kasar dake da karfin tattalin arziki a Duniya dama Afrika

  22/06/2019 Duración: 19min

  A cikin wannan shirin, zaku ji kasar da ke kan gaba a tattalin arziki a duniya da ma Afirka, a wannan shekarar ta 2019. Banda haka Mickael Kuduson ya duba tambaya da ta shafi kasar Libya.

 • Tambaya da Amsa - Karin haske dangane da mafarki

  Tambaya da Amsa - Karin haske dangane da mafarki

  15/06/2019 Duración: 19min

  A cikin shirin Tambaya da amsa ,Mickael Kuduson ya mayar da hankali zuwa ga wasu daga cikin tambayoyin masu saurare da suka bukaci samun karin haske dangane da mafarki.  

 • Tambaya da Amsa - Tarihin gidan kaso na Koutukale dake Nijar

  Tambaya da Amsa - Tarihin gidan kaso na Koutukale dake Nijar

  08/06/2019 Duración: 19min

  A cikin shirin Tambaya da Amsa,masu saurare sun bukaci samu karin haske da kuma tarihin gidan kaso na Koutoukale dake Jamhuriyar Nijar,dangane da haka  Souley Maje Rejeto daga Nijar  ya taimaka a haka. Shirin tambaya da amsa tareda Mickael Kuduson.

 • Tambaya da Amsa - Bayani kan Aladar nan ta (Tashe) A kasar Hausa

  Tambaya da Amsa - Bayani kan Al'adar nan ta (Tashe) A kasar Hausa

  01/06/2019 Duración: 19min

  A cikin shirin tambaya da Amsa Mickael Kuduson ya mayar da hankali domin kai tambayoyin ku zuwa masana tarihi ,daga cikin tambayoyin na ku ,za mu iya duba wacce ta shafi batun tashe daya daga cikin al'adun kasashen hausa. Sai ku biyo mu.  

 • Tambaya da Amsa - Shin ko gwamna na da hurumin kirkiro masarauta?

  Tambaya da Amsa - Shin ko gwamna na da hurumin kirkiro masarauta?

  18/05/2019 Duración: 19min

   A cikin shirin na yau,za a ji ko shin  Gwamnan jiha na da hurumin kirkiro da masarautu kuma idan ya kirkiro sun zauna kenan har abada abadin? A cikin shirin tambaya da amsa Mickael Kuduson ya samu tattaunawa da masana da suka kawo na su sani a kai.

 • Tambaya da Amsa - Ci gaban amsa kan tarihin tsohon shugaban kasar Sudan Omar Hassan al-Bashir

  Tambaya da Amsa - Ci gaban amsa kan tarihin tsohon shugaban kasar Sudan Omar Hassan al-Bashir

  04/05/2019 Duración: 19min

  A cikin shirin tambaya da amsa na yau tare da Micheal Kuduson za ku ji ci gaban tarihin gwagwarmayar hambararren shugaban kasar Sudan Omar Hassan al Bashir dama ci gaban tarihin kwamishinan 'yan sandan jihar Kano tare da karin amsoshin wasu tambayoyi ayi saurare lafiya.

 • Tambaya da Amsa - Tarihin Omar Hassan al-Bashir hambararren shugaban kasar Sudan

  Tambaya da Amsa - Tarihin Omar Hassan al-Bashir hambararren shugaban kasar Sudan

  27/04/2019 Duración: 19min

  A cikin shirin tambaya da amsa na yau Asabar tare da Micheal Kuduson za su amsar tambayoyin da suka hadar da tarihin shugaba Omar Hassan al-Bashir na Sudan da tarihin fara amfani da na'urar taimakawa alkalin wasa ta VAR a fagen kwallo da ma karashen tattaunawarsu da kwamishinan 'yan sandan jihar Kano CP Muhammad Wakil. A yi sauraro lafiya.

 • Tambaya da Amsa - Amsoshin tambayoyin ku masu saurare daga RFI

  Tambaya da Amsa - Amsoshin tambayoyin ku masu saurare daga RFI

  20/04/2019 Duración: 20min

  Shirin amsa tambayoyin da masu sauraro suka aiko mana da su, inda muke yin duk mai yiwuwa wajen samar da amsoshin da suka dace, Kamar kowane mako, haka zalika a wannan makon Michael Kuduson ke muku lale marhabun.

 • Tambaya da Amsa - Amsoshin tambayoyin ku masu saurare daga RFI

  Tambaya da Amsa - Amsoshin tambayoyin ku masu saurare daga RFI

  13/04/2019 Duración: 20min

  A cikin shirin tambayoyin ku masu saurare,Mikael Kuduson ya duba wasu daga cikin tambayoyi da ya mika zuwa masana domin gamsar da mai saurare. Shirin Tambaya da amsa daga nan sashen Hausa na Rediyon Faransa International.

 • Tambaya da Amsa - Ko kaho da wanzamai ke yi na da alfanu ko akasin haka?

  Tambaya da Amsa - Ko kaho da wanzamai ke yi na da alfanu ko akasin haka?

  07/04/2019 Duración: 19min

  Shiri ne da ke amsa tambayoyin masu sauraro kamar yadda suka aiko mana, kuma yake zuwa muku duk mako,ta sashen Hausa na Radio France Internationale, naku, Michael Kuduson ke cewa a yi sauraro lafiya. Sani Mailengelenge, Yelwa Yauri a jihar Kebbin Najeriya, ya ce a tambaya mana likita ko kaho da wanzamai ke yi na da alfanu ko akasin haka? Ko akwai abin da yayi kama da kaho a likitance?

 • Tambaya da Amsa - Karin bayani kan tsarin rashin kammaluwar zabe na Inconclusive a Turance

  Tambaya da Amsa - Karin bayani kan tsarin rashin kammaluwar zabe na Inconclusive a Turance

  31/03/2019 Duración: 19min

  Shirin Tambaya da Amsa kamar yadda aka saba, ya amsa wasu tambayoyin da masu sauraro suka aiko, daga cikinsu kuma akwai neman karin bayani kan tsarin rashin kammaluwar zabe a Najeriya na Incoclusive a Turance.

 • Tambaya da Amsa - Makomar Jamian tsaro yayin gudanar da zabuka dangane da kada nasu kuriun

  Tambaya da Amsa - Makomar Jami'an tsaro yayin gudanar da zabuka dangane da kada nasu kuri'un

  25/03/2019 Duración: 20min

  Shirin Tambaya da Amsa na wannan makon yayi karin haske kan makomar jami'an tsaron yayin kada kuri'a a zabukan Najeriya, la'akari da cewa ana tafka muhawara kan ko sauran jama'ar kasa sun wakilci, ma'ana ba dole bane sai sun kada tasu kuri'ar. Zalika shirin ya ji ta bakin masu ruwa da tsaki kan ajin mutanen da zabe ya haramta a garesu. Kamar yadda aka saba dai shirin Tambaya da Amsa ya kuma tuntubi masana don karin bayani akan wasu tambayoyin da masu sauraro suka aiko mana.  

 • Tarihin mawaki, Alpha Blondy

  Tarihin mawaki, Alpha Blondy

  02/03/2019 Duración: 20h01min

  An haifi Alpha Blondy a ranar 1 ga watan Janairun shekarar 1953 a garin Dimbokro na kasar Ivory Coast. Mawaki ne da yake waka da salon Reggae,wato Reggae Music. Sunansa Seydou Koné, Mickael Kuduson ya duba mana tarihin sa a cikin shirin amsar tambayoyin masu saurare.

 • Bambancin da ke tsakanin tsarin mulkin gurguzu, jari hujja, da dimokuradiyya

  Bambancin da ke tsakanin tsarin mulkin gurguzu, jari hujja, da dimokuradiyya

  26/01/2019 Duración: 19min

  A cikin shirin tambaya da amsa Mickael Kudson ya mayar da hankali zuwa wasu daga cikin tambayoyin masu saurare,Hussaini Abba Dambam da Muhammad Musa Dambam, ‘ya'an Malam Musa Mai Gyaran Keke Karamar Hukumar Dambam a jihar Bauchin Najeriya, Suka ce shin,idan aka wa wasu operation wato tiyata sai ka ga wurin yayi ciwo yana ruwa, yaya kuma za a kauce wa haka?

 • Dalilan da suka haddasa takaddama kan ficewar Birtaniya daga cikin EU

  Dalilan da suka haddasa takaddama kan ficewar Birtaniya daga cikin EU

  19/01/2019 Duración: 20h04min

  Shirin Tambaya da Amsa na wannan makon kamar yadda ya saba, ya amsa wasu daga cikin tambayoyin da masu sauraro suka nemi karin bayani akansu, daga cikin tambayoyin kuma akwai neman cikakken bayani kan dalilan da suka haddasa takaddama kan batun ficewar Birtaniya da cikin kungiyar EU.

 • Faduwar hannayen jari a kasuwannin Duniya

  Faduwar hannayen jari a kasuwannin Duniya

  12/01/2019 Duración: 20h06min

  Tambaya Da Amsa, shiri ne da ke wayar wa da mai sauraro kai game da lammuran da suka shige musu duhu a kowane fanni na rayuwa, kuma yake zuwa muku daga rediyon Faransa International Rfi hausa tareda MICHAEL KUDUSON.

página 2 de 5