Tambaya Da Amsa

Tambaya Da Amsa

Sinopsis

Masu Saurare na aiko da Tambayoyinsu domin neman amsa a shirin, Ana gabatar da shirin ne a karshen mako.

Quién oyó esto, también escuchó:


Episodios

 • Tambaya da Amsa - Maanar G5 da yankin Sahel
  Tambaya da Amsa - Ma'anar G5 da yankin Sahel
  Duración: 20min | 25/01/2020

  Masu sauraren Rfi Hausa ,sun nemi a basu karin haske dangane da Yankin G5 Sahel wane yanki ake kira Sahel shin kasashe nawa ne a cikin wannan yankin kuma a ina ya samo wannan suna? Mickael Kuduson a cikin shirin tambaya da amsa ya jiyo ta bakin masana dangane da wadana tambayoyi daga masu saurare a cikin shirin tambaya da Amsa daga nan sashen hausa na Rfi.

 • Tambaya da Amsa - Tarihin Shahararren Mawakin nan Abubakar Mai Bibbiyu
  Tambaya da Amsa - Tarihin Shahararren Mawakin nan Abubakar Mai Bibbiyu
  Duración: 19min | 18/01/2020

  Gambo Damagaram da Wari Malam Bare Barezuwa da Bamaini Hannami Mormotuwa duka Jamhuriya Nijar. Tarihin Shararran Mawakin nan Abubakar Mai Bibbiyu suke nema,Mickael Kuduson ya duba tambaya ,ga kuma hirar da ya samu da Abubakar Mai Bibbiyu cikin shirin tambaya da amsa.

 • Tambaya da Amsa - Alfanun shan nonon rakumi
  Tambaya da Amsa - Alfanun shan nonon rakumi
  Duración: 19min | 28/12/2019

  A cikin shirin tambaya da amsa ,wasu daga cikin masu saurare sun bukaci samun karin haske dangane da alfanun shan nonon rakumi. Mickael Kuduson ya jiyo ta baki masana ,da suka duba wasu daga cikin tambayoyin ku masu sauraren RFI a cikin wannan shirin.

 • Tambaya da Amsa - Amsar tambaya kan alakar sanyin hunturu da karuwar masu tabin hankali
  Tambaya da Amsa - Amsar tambaya kan alakar sanyin hunturu da karuwar masu tabin hankali
  Duración: 19min | 21/12/2019

  Shirin Tambaya da amsa a wannan makon tare da Michael Kuduson ya amsa muhimman tambayoyi ciki har da tambayar da ke neman karin bayani kan alakar yawaitar samun masu tabin hankali a lokacin hunturu.

 • Tambaya da Amsa - Aman wuta daga dutse cikin ruwa?
  Tambaya da Amsa - Aman wuta daga dutse cikin ruwa?
  Duración: 19min | 14/12/2019

  A cikin shirin tambaya da Amsa, za ku ji ko a ina aka kwana dangane da wasu daga cikin matsalolli da suka jibanci kiwon lafiya,musaman shan suga daga dan Adam, wasu daga cikin masu saurare sun nemi ji ko mai ya sa ake samun aman wuta daga dutse cikin ruwa. Mickael Kuduson ya ji ta bakin masana a cikin shirin tambaya da Amsa.

 • Tambaya da Amsa - Amsar tambaya kan matsayin yankin Hong Kong mai kwarya-kwaryar yancin karkashin China
  Tambaya da Amsa - Amsar tambaya kan matsayin yankin Hong Kong mai kwarya-kwaryar 'yancin karkashin China
  Duración: 19min | 07/12/2019

  Shirin Tambaya da Amsa na wannan makon tare da Micheal Kuduson ya amsa muhimman tambayoyi ga masu sauraro ciki har da matsayin yankin Hong Kong ga gwamnatin China.

 • Tambaya da Amsa - Amsar Tambaya kan alfanun wanka da ruwan zafi ga jikin dan adam
  Tambaya da Amsa - Amsar Tambaya kan alfanun wanka da ruwan zafi ga jikin dan adam
  Duración: 20min | 30/11/2019

  Shirin Tambaya da Amsa a wannan lokaci ya amsa muhimman tambayoyin da kuka aiko mana ciki har da tambayar da ke neman sanin muhimmancin amfani da ruwan zafi ga lafiyar bil'adama. Ayi saurare Lafiya.

 • Tambaya da Amsa - Adam A Zango ya amsa wasu daga cikin tambayoyin RFI
  Tambaya da Amsa - Adam A Zango ya amsa wasu daga cikin tambayoyin RFI
  Duración: 20min | 23/11/2019

  A cikin shirin tambayoyin ku masu saurare,Mickael Kuduson ya nemi jin ta bakin masana da ya dace su kawo muku karin haske dangane da wasu daga cikin tambayoyin da kuka aiko. Haka zalika zaku ji hirar darediyon Faransa na rfi yayi da Adam A Zango.

 • Tambaya da Amsa - Karin bayani kan kan rabe-raben aikin hako mai a sassan Najeriya
  Tambaya da Amsa - Karin bayani kan kan rabe-raben aikin hako mai a sassan Najeriya
  Duración: 20min | 16/11/2019

  Shirin Tambaya da Amsa a wannan makon ya tattauna da masana kan batutuwan da masu sauraro suka nemi karin haske akai, ciki har da karin bayani kan rabe-raben aikin hako mai a sassan Najeriya, da kuma tasiri rufe kan iyakokin kasa da kuma kasashen da suka yi amfani da salon wajen karfafa tattalin arzikinsu.

 • Tambaya da Amsa - Rikicin siyasa
  Tambaya da Amsa - Rikicin siyasa
  Duración: 19min | 09/11/2019

  An taba samu wanda ya kalubalanci sakamakon zabe a tarihin Najeriya har ya kai ga zuwa kotu kamar yadda Atiku Abubakar ke yi? Idan har an taba, ya aka kare? Shin a wane irin kotu ake kai wannan korafi? Mickael Kuduson ya duba wasu daga cikin tambayoyi masu saurare,tareda duba amsoshin su da masana.

 • Tambaya da Amsa - Karin bayani kan manhajar Google Play Store
  Tambaya da Amsa - Karin bayani kan manhajar 'Google Play Store'
  Duración: 19min | 26/10/2019

  Shirin Tambaya da Amsa na wannan makon yayi karin bayani kan batutuwa da dama dangane da  manhajar 'Google Play Store', sai kuma wasu karin tambayoyin da masu sauraro suka aiko.

 • Tambaya da Amsa - Amsar Tambaya kan manhajar kudi ta Intanet wato Crypto currency
  Tambaya da Amsa - Amsar Tambaya kan manhajar kudi ta Intanet wato Crypto currency
  Duración: 19min | 19/10/2019

  Shirin Tambaya da amsa tare da Micheal Kuduson ya amsa manyan tambayoyo ciki har da karin bayani kan manhajar kudin intanet na Crypto currency. Ayi saurare Lafiya.

 • Tambaya da Amsa - Kabila guda ce Tuareq da Buzaye Da kuma Abzinawa?
  Tambaya da Amsa - Kabila guda ce Tuareq da Buzaye Da kuma Abzinawa?
  Duración: 19min | 12/10/2019

  A cikin shirin Amsa da tambaya daga nan sashen hausa na rediyon Faransa Mickael Kuduson ya mayar da hankali zuwa wasu daga cikin tambayoyin ku masu saurare kamar haka: Kabila guda ce Tuareq da Buzaye da kuma Abzinawa? Wace dangantaka wadannan kabilu keda shi da larabawa? Shin bayan wadannan akwai wasu kabilun farar fata wadanda ba larabawa ba a kasashen Afrika.

 • Tambaya da Amsa - Dalilan dake haddasa jinkiri da rashin haihuwa
  Tambaya da Amsa - Dalilan dake haddasa jinkiri da rashin haihuwa
  Duración: 19min | 05/10/2019

  Shirin Tambaya da Amsa kamar yadda aka saba, ya amsa wasu tambayoyi da masu sauraro suka aiko, ciki har da neman karin bayani kan dalilan da suke haddasa matsalar jinkirin samun haihuwa da rashin ma baki daya.

 • Tambaya da Amsa - Dalilan rikicin kyamar baki a Afrika ta Kudu
  Tambaya da Amsa - Dalilan rikicin kyamar baki a Afrika ta Kudu
  Duración: 20min | 21/09/2019

  Shirin Tambaya da Amsa kamar yadda aka saba, ya amsa wasu tambayoyi da masu sauraro suka aiko, ciki har da neman karin bayani kan dalilan matsalar kyamar baki a kasar Afrika ta Kudu.

 • Tambaya da Amsa - Cikakkiyar maanar juyin-juye hali
  Tambaya da Amsa - Cikakkiyar ma'anar juyin-juye hali
  Duración: 19min | 31/08/2019

  A cikin shirin tambayoyin da za ku ji amshoshin wasu daga cikin tambayoyin ku,wasu masu saurare sun bukaci sanin cikakkiyar ma'anar juyin-juye hali,ribarsa da illarsa da saurensu. Mickael Kuduson ya bincika tareda samu amsar wadanan tambayoyi.

 • Tambaya da Amsa - Amsar Tambaya kan kasashen da ke da kujeran naki a Majalisar Dinkin Duniya
  Tambaya da Amsa - Amsar Tambaya kan kasashen da ke da kujeran naki a Majalisar Dinkin Duniya
  Duración: 19min | 24/08/2019

  Shirin Tambaya da Amsa tare da Micheal Kuduson ya amsa muhimman tambayoyi a wannan mako, ciki har da amsar tambayar kasashen da ke da kujerar naki a Majalisar Dinkin Duniya, Ayi saurare Lafiya.

 • Tambaya da Amsa - Karin haske kan mutuwar Osama bin Laden da kuma alakarsa da Amurka
  Tambaya da Amsa - Karin haske kan mutuwar Osama bin Laden da kuma alakarsa da Amurka
  Duración: 19min | 17/08/2019

  Shirin Tambaya da Amsa kamar, ya amsa wasu tambayoyi da masu sauraro suka aiko, ciki har da mutuwar Osama bin Laden da kuma alakarsa da Amurka, sai kuma bayani kan juyin juya hali, manufarsa, illoli da kuma amfaninsa.

 • Tambaya da Amsa - Amsar Tambayar dalilan da suka haddasa rikicin kasar Rwanda
  Tambaya da Amsa - Amsar Tambayar dalilan da suka haddasa rikicin kasar Rwanda
  Duración: 20min | 03/08/2019

  Shirin Tambaya da amsa na wannan mako tare da Micheal Kuduson, ya bayar da amsa kan tambayar da ke neman sanin dalilan da suka haddasa rikicin kasar Rwanda shekaru kusan 25 da suka gabata, wannan dama sauran muhimman tambayoyi da amsa na tattare a cikin shirin, a yi saurare lafiya.

 • Tambaya da Amsa - Likita ya amsa wasu daga ciki tambayoyi da suka shafi mata
  Tambaya da Amsa - Likita ya amsa wasu daga ciki tambayoyi da suka shafi mata
  Duración: 19min | 27/07/2019

  A cikin shirin Tambaya da amsa,likita ya amsa wasu daga cikin tambayoyi da suka jibanci lafiyar  mace mai dauke da juna biyu,banda haka zaku ji koa ina aka kwana dangane da tarihin yan tagwaye dake magane kamar Shugaba Buhari a Najeriya.

 • Tambaya da Amsa - Shirin Tambaya da Amsa tare da Micheal Kuduson 20-07-2019
  Tambaya da Amsa - Shirin Tambaya da Amsa tare da Micheal Kuduson 20-07-2019
  Duración: 20min | 20/07/2019

  Shirin Tambaya da amsa tare da Micheal kuduson ya amsa muhimman tambayoyi tare da tuntubar masana daga fannoni daban-daban,ciki kuwa har da matakan da aka bi wajen damkawa Jamhuriyar Kamaru yankin Bakassi. ayi saurare lafiya.

 • Tambaya da Amsa - Aikin lauya a Najeriya ,da kuma hanyoyin samu lambar girma ta SAN
  Tambaya da Amsa - Aikin lauya a Najeriya ,da kuma hanyoyin samu lambar girma ta SAN
  Duración: 19min | 13/07/2019

  Mahmud Salihu Kaura Namoda, jihar Zamfara a tarayyar Najeriya, so yake a mai bayanin yadda lauya a Najeriya ke iya zama babban lauyan kasa mai lambar girmamawa ta SAN. Mickael Kuduson ya duba wasu daga cikin tambayoyin masu saurare.

 • Tambaya da Amsa - Tsarin yadda za a rika amfani da kudin bai-daya na kasashen ECOWAS
  Tambaya da Amsa - Tsarin yadda za a rika amfani da kudin bai-daya na kasashen ECOWAS
  Duración: 19min | 06/07/2019

  Shirin Tambaya da Amsa na wannan makon ya tuntubi masana dangane da wasu daga cikin batutuwan da masu sauraro suka nemi karin bayani akai, da suka hada da bayani kan tsarin yadda za a rika amfani da kudin bai-daya na kasashen ECOWAS, sai kuma dalilan rikicin Amurka da Iran, da kuma kasashen da rikicin zai shafa.

 • Tambaya da Amsa - Dalilan da ke sanya kai harin Intanet dama wadanda suka fara kai harin a tarihi
  Tambaya da Amsa - Dalilan da ke sanya kai harin Intanet dama wadanda suka fara kai harin a tarihi
  Duración: 26min | 29/06/2019

  A cikin shirin Tambaya da Amsa tare da Micheal Kuduson na wannan mako za su amshi tambayoyin da suka hada da dalilan da kan sanya kakabawa kasa takunkumi, tarihi fara kai harin Intanet da ma kasar da ta fara kai shi, da dai sauran amsoshin tambayoyin da ku masu saurare kuka aiko man. Asha saurare Lafiya.

 • Tambaya da Amsa - Kasar dake da karfin tattalin arziki a Duniya dama Afrika
  Tambaya da Amsa - Kasar dake da karfin tattalin arziki a Duniya dama Afrika
  Duración: 19min | 22/06/2019

  A cikin wannan shirin, zaku ji kasar da ke kan gaba a tattalin arziki a duniya da ma Afirka, a wannan shekarar ta 2019. Banda haka Mickael Kuduson ya duba tambaya da ta shafi kasar Libya.

 • Tambaya da Amsa - Karin haske dangane da mafarki
  Tambaya da Amsa - Karin haske dangane da mafarki
  Duración: 19min | 15/06/2019

  A cikin shirin Tambaya da amsa ,Mickael Kuduson ya mayar da hankali zuwa ga wasu daga cikin tambayoyin masu saurare da suka bukaci samun karin haske dangane da mafarki.  

 • Tambaya da Amsa - Tarihin gidan kaso na Koutukale dake Nijar
  Tambaya da Amsa - Tarihin gidan kaso na Koutukale dake Nijar
  Duración: 19min | 08/06/2019

  A cikin shirin Tambaya da Amsa,masu saurare sun bukaci samu karin haske da kuma tarihin gidan kaso na Koutoukale dake Jamhuriyar Nijar,dangane da haka  Souley Maje Rejeto daga Nijar  ya taimaka a haka. Shirin tambaya da amsa tareda Mickael Kuduson.

 • Tambaya da Amsa - Bayani kan Aladar nan ta (Tashe) A kasar Hausa
  Tambaya da Amsa - Bayani kan Al'adar nan ta (Tashe) A kasar Hausa
  Duración: 19min | 01/06/2019

  A cikin shirin tambaya da Amsa Mickael Kuduson ya mayar da hankali domin kai tambayoyin ku zuwa masana tarihi ,daga cikin tambayoyin na ku ,za mu iya duba wacce ta shafi batun tashe daya daga cikin al'adun kasashen hausa. Sai ku biyo mu.  

 • Tambaya da Amsa - Shin ko gwamna na da hurumin kirkiro masarauta?
  Tambaya da Amsa - Shin ko gwamna na da hurumin kirkiro masarauta?
  Duración: 19min | 18/05/2019

   A cikin shirin na yau,za a ji ko shin  Gwamnan jiha na da hurumin kirkiro da masarautu kuma idan ya kirkiro sun zauna kenan har abada abadin? A cikin shirin tambaya da amsa Mickael Kuduson ya samu tattaunawa da masana da suka kawo na su sani a kai.

 • Tambaya da Amsa - Ci gaban amsa kan tarihin tsohon shugaban kasar Sudan Omar Hassan al-Bashir
  Tambaya da Amsa - Ci gaban amsa kan tarihin tsohon shugaban kasar Sudan Omar Hassan al-Bashir
  Duración: 19min | 04/05/2019

  A cikin shirin tambaya da amsa na yau tare da Micheal Kuduson za ku ji ci gaban tarihin gwagwarmayar hambararren shugaban kasar Sudan Omar Hassan al Bashir dama ci gaban tarihin kwamishinan 'yan sandan jihar Kano tare da karin amsoshin wasu tambayoyi ayi saurare lafiya.

 • Tambaya da Amsa - Tarihin Omar Hassan al-Bashir hambararren shugaban kasar Sudan
  Tambaya da Amsa - Tarihin Omar Hassan al-Bashir hambararren shugaban kasar Sudan
  Duración: 19min | 27/04/2019

  A cikin shirin tambaya da amsa na yau Asabar tare da Micheal Kuduson za su amsar tambayoyin da suka hadar da tarihin shugaba Omar Hassan al-Bashir na Sudan da tarihin fara amfani da na'urar taimakawa alkalin wasa ta VAR a fagen kwallo da ma karashen tattaunawarsu da kwamishinan 'yan sandan jihar Kano CP Muhammad Wakil. A yi sauraro lafiya.

 • Tambaya da Amsa - Amsoshin tambayoyin ku masu saurare daga RFI
  Tambaya da Amsa - Amsoshin tambayoyin ku masu saurare daga RFI
  Duración: 20min | 20/04/2019

  Shirin amsa tambayoyin da masu sauraro suka aiko mana da su, inda muke yin duk mai yiwuwa wajen samar da amsoshin da suka dace, Kamar kowane mako, haka zalika a wannan makon Michael Kuduson ke muku lale marhabun.

 • Tambaya da Amsa - Amsoshin tambayoyin ku masu saurare daga RFI
  Tambaya da Amsa - Amsoshin tambayoyin ku masu saurare daga RFI
  Duración: 20min | 13/04/2019

  A cikin shirin tambayoyin ku masu saurare,Mikael Kuduson ya duba wasu daga cikin tambayoyi da ya mika zuwa masana domin gamsar da mai saurare. Shirin Tambaya da amsa daga nan sashen Hausa na Rediyon Faransa International.

 • Tambaya da Amsa - Ko kaho da wanzamai ke yi na da alfanu ko akasin haka?
  Tambaya da Amsa - Ko kaho da wanzamai ke yi na da alfanu ko akasin haka?
  Duración: 19min | 07/04/2019

  Shiri ne da ke amsa tambayoyin masu sauraro kamar yadda suka aiko mana, kuma yake zuwa muku duk mako,ta sashen Hausa na Radio France Internationale, naku, Michael Kuduson ke cewa a yi sauraro lafiya. Sani Mailengelenge, Yelwa Yauri a jihar Kebbin Najeriya, ya ce a tambaya mana likita ko kaho da wanzamai ke yi na da alfanu ko akasin haka? Ko akwai abin da yayi kama da kaho a likitance?

 • Tambaya da Amsa - Karin bayani kan tsarin rashin kammaluwar zabe na Inconclusive a Turance
  Tambaya da Amsa - Karin bayani kan tsarin rashin kammaluwar zabe na Inconclusive a Turance
  Duración: 19min | 31/03/2019

  Shirin Tambaya da Amsa kamar yadda aka saba, ya amsa wasu tambayoyin da masu sauraro suka aiko, daga cikinsu kuma akwai neman karin bayani kan tsarin rashin kammaluwar zabe a Najeriya na Incoclusive a Turance.

 • Tambaya da Amsa - Makomar Jamian tsaro yayin gudanar da zabuka dangane da kada nasu kuriun
  Tambaya da Amsa - Makomar Jami'an tsaro yayin gudanar da zabuka dangane da kada nasu kuri'un
  Duración: 20min | 25/03/2019

  Shirin Tambaya da Amsa na wannan makon yayi karin haske kan makomar jami'an tsaron yayin kada kuri'a a zabukan Najeriya, la'akari da cewa ana tafka muhawara kan ko sauran jama'ar kasa sun wakilci, ma'ana ba dole bane sai sun kada tasu kuri'ar. Zalika shirin ya ji ta bakin masu ruwa da tsaki kan ajin mutanen da zabe ya haramta a garesu. Kamar yadda aka saba dai shirin Tambaya da Amsa ya kuma tuntubi masana don karin bayani akan wasu tambayoyin da masu sauraro suka aiko mana.  

 • Tarihin mawaki, Alpha Blondy
  Tarihin mawaki, Alpha Blondy
  Duración: 20h01min | 02/03/2019

  An haifi Alpha Blondy a ranar 1 ga watan Janairun shekarar 1953 a garin Dimbokro na kasar Ivory Coast. Mawaki ne da yake waka da salon Reggae,wato Reggae Music. Sunansa Seydou Koné, Mickael Kuduson ya duba mana tarihin sa a cikin shirin amsar tambayoyin masu saurare.

 • Bambancin da ke tsakanin tsarin mulkin gurguzu, jari hujja, da dimokuradiyya
  Bambancin da ke tsakanin tsarin mulkin gurguzu, jari hujja, da dimokuradiyya
  Duración: 19min | 26/01/2019

  A cikin shirin tambaya da amsa Mickael Kudson ya mayar da hankali zuwa wasu daga cikin tambayoyin masu saurare,Hussaini Abba Dambam da Muhammad Musa Dambam, ‘ya'an Malam Musa Mai Gyaran Keke Karamar Hukumar Dambam a jihar Bauchin Najeriya, Suka ce shin,idan aka wa wasu operation wato tiyata sai ka ga wurin yayi ciwo yana ruwa, yaya kuma za a kauce wa haka?

 • Dalilan da suka haddasa takaddama kan ficewar Birtaniya daga cikin EU
  Dalilan da suka haddasa takaddama kan ficewar Birtaniya daga cikin EU
  Duración: 20h04min | 19/01/2019

  Shirin Tambaya da Amsa na wannan makon kamar yadda ya saba, ya amsa wasu daga cikin tambayoyin da masu sauraro suka nemi karin bayani akansu, daga cikin tambayoyin kuma akwai neman cikakken bayani kan dalilan da suka haddasa takaddama kan batun ficewar Birtaniya da cikin kungiyar EU.

 • Faduwar hannayen jari a kasuwannin Duniya
  Faduwar hannayen jari a kasuwannin Duniya
  Duración: 20h06min | 12/01/2019

  Tambaya Da Amsa, shiri ne da ke wayar wa da mai sauraro kai game da lammuran da suka shige musu duhu a kowane fanni na rayuwa, kuma yake zuwa muku daga rediyon Faransa International Rfi hausa tareda MICHAEL KUDUSON.

 • Amfanin da ke tattare da samar da kudin bai daya tsakanin kasashen Afrika
  Amfanin da ke tattare da samar da kudin bai daya tsakanin kasashen Afrika
  Duración: 21h06min | 29/12/2018

  Shirin Tambaya da Amsa na wannan makon ya nemi jin karin bayani daga masana kan wasu tambayoyin da masu sauraro suka aiko; daga cikin tambayoyin akwai neman sanin amfanin da ke tattare da samar da kudin bai daya tsakanin kasashen yammacin Afrika, sai kuma 'banbanci tsakanin yaron da aka yi wa shayi yana jariri da kuma wanda aka yi masa bayan ya girma.

 • Tarihin Sashin Hausa na Radio France International
  Tarihin Sashin Hausa na Radio France International
  Duración: 19min | 22/12/2018

  Shirin Tambaya da Amsa na wannan mako ya bada tarihin kafuwar Sashin Hausa na RFI kamar yadda wasu daga cikin masu sauraro suka bukata. Shirin ya kuma amsa wasu daga cikin tambayoyin da masu sauraro suka aiko.

 • Karin bayani kan canji da dumamar yanayi da kuma illolinsa
  Karin bayani kan canji da dumamar yanayi da kuma illolinsa
  Duración: 19min | 15/12/2018

  Shirin Tambaya da Amsa na wannan mako kamar yadda aka saba ya amsa wasu daga cikin tambayoyin da masu sauraro suka nemi karin bayani akansu, daga cikin tambayoyin akwai illolin canjin yanayi da dalilansa, sai kuma tarihin Masarautar Musulunci ta Jinju dake Jamhuriyar Nijar.

 • Hanyoyin magance kamuwa da ciwon hakori
  Hanyoyin magance kamuwa da ciwon hakori
  Duración: 20min | 01/12/2018

  Shirin Tambaya da Amsa na wannan makon ya dora ne bisa amsa wasu daga cikin tambayoyin da masu sauraro suka aiko domin neman karin bayani. Wasu daga cikin jerin tambayoyin da shirin na wannan mako yayi karin haske akai sun hada da matsalar ciwon hakori da yadda za'a magance shi, sai kuma karin bayani akan al'adar gada.

 • Karin haske dangane da ciwon Suga
  Karin haske dangane da ciwon Suga
  Duración: 20min | 24/11/2018

  A cikin shirin tambaya da amsa,Souley Maje Rejeto ya mayar da hankali tareda samun karin haske daga likitoci dangane da ciwon Suga,tareda duba wasu daga cikin tambayoyin ku masu sauraren RFI hausa.

 • Tarihin Jamal Kashoggi
  Tarihin Jamal Kashoggi
  Duración: 19min | 10/11/2018

  Shirin Tambaya da Amsa kamar yadda aka saba ya yi karin bayani kan wasu daga cikin tambayoyin da masu sauraro suka aiko, ta hanyar tattaunawa da masana kan fannin da aka nemi sani a kansa. Daga cikin tambayoyin da aka amsa a wannan mako akwai Tarihin Jamal Kashoggi dan jaridar kuma dan asalin Saudiya da aka yiwa kisan gilla a ofishin jakadancin kasar ta Saudiya dake birnin Istanbul na Turkiya.

 • Menene Kambun Baka
  Menene Kambun Baka
  Duración: 19min | 03/11/2018

  Cikin wannan shiri wanda Michael Kuduson ya gabatar za'a ji cikakken bayani dangane da kalmar  dokat ta baci da dokar takaita zirga-zirga. Sai ayi sauraro lafiya.

 • Kasashen renon Faransa ba sa gudanar da zaben gwamnoni sai na Shugaban kasa
  Kasashen renon Faransa ba sa gudanar da zaben gwamnoni sai na Shugaban kasa
  Duración: 19min | 20/10/2018

  Kusan akasarin kasashen renon Faransa ,kamar su Jamhuriyar Nijar da Kamaru da sauransu ba sa gudanar da zaben  gwamnoni sai na Shugaban kasa? Sai dai ka ji Gwamnan kaza,gwamnan kaza,to ko ya suke darewa kan mulki? Michael Kudson  a cikin shirin tambaya da amsa ya dubo wasu amsoshin tambayoyin ku masu saurare.

 • Karin bayani a kan Dodo
  Karin bayani a kan Dodo
  Duración: 19min | 13/10/2018

  Shirin tambaya da amsa ya na duba tambayoyi daga masu sauraro,kana ya na samar da amsoshi kamar yadda suka sawwaka. A cikin shirin na wannan lokaci Michael Kudson zai duba wasu daga cikin tambayoyi daga masu sauraro.

 • Masana Sun Yi Bayani Game Da Mahaukaciyar Iska
  Masana Sun Yi Bayani Game Da Mahaukaciyar Iska
  Duración: 19min | 06/10/2018

  Cikin wannan shiri na Tambaya da Amsa da Michael Kuduson zai gabatar za'a ji bayanin masana game da mahaukaciyar iska da goguwa dake barna a wasu kasashen duniya.

 • Karin bayani akan Manhajar zamani ta Taswirar duniya Google Map
  Karin bayani akan Manhajar zamani ta Taswirar duniya 'Google Map'
  Duración: 19min | 29/09/2018

  Shirin Tambaya da Amsa na wannan makon ya nemo amsoshin wasu daga cikin tambayoyin da masu sauraro kuka aiko, kamar yadda aka saba. Daga cikin tambayoyin akwai karin bayani akan Manhajar zamani ta Taswirar duniya 'Google Map'

 • Bayani kan shekarar da aka haramta amfani da makaman nukiliya da kuma kasashen da suka taba amfani da su
  Bayani kan shekarar da aka haramta amfani da makaman nukiliya da kuma kasashen da suka taba amfani da su
  Duración: 19min | 22/09/2018

  Shirin Tambaya da Amsa na wannan makon, kamar yadda ya saba, ya duba wasu daga cikin tambayoyin da masu sauraro suka aiko don neman karin bayani, daga ciki kuma akwai neman karin haske akan lokacin da soma haramta amfani da makaman nukiliya, da kuma kasashen da suka taba yin amfani da su.

 • Bayani game da matsalar tattalin arzikin kasar Venezuela
  Bayani game da matsalar tattalin arzikin kasar Venezuela
  Duración: 19min | 15/09/2018

  Cikin wannan shiri wanda Micheal Kuduson yake gabatarwa za'a ji bayani game da sukurkucewar darajar tattalin arzikin kasar Venezuela, za'a  kuma aji banbancin motsin kasa da girgizan kasa. Sai ayi sauraro lafiya.

 • Tambaya da amsa, tare da Michael Kuduson
  Tambaya da amsa, tare da Michael Kuduson
  Duración: 19min | 08/09/2018

  A tare da Michael Kuduson, shirin Tambaya da Amsa na wannan mako ya amsa tambayoyin masu saurare ne cikin har da wadda ke neman sanin asalin ''karin magana '' da Hausawa ke yi.

 • Rayuwar Koffi Annan
  Rayuwar Koffi Annan
  Duración: 20min | 01/09/2018

  Bayan mukamin Sakataren Majalisar Dinkin Duniya,ya kasance manzo na  musamman na Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar Kasashen larabawa wajen warware rikicin siyasar kasar Syria,Koffi Annan,masu saurare sun bukaci samun labari da tarihin sa. Sai ku biyo mu cikin shirin amsoshin ku masu saurare.

 • Dalilan da ke haddasa dumamar yanayi ko tsananin zafi a sassan duniya
  Dalilan da ke haddasa dumamar yanayi ko tsananin zafi a sassan duniya
  Duración: 19h01min | 18/08/2018

  Shirin 'Tambaya da Amsa' na wannan makon wanda Shamsiyya Hamza Ibrahim ta gabatar, ya amsa wasu daga cikin tambayoyin da masu sauraro suka nemi a amsa musu. Daga cikin tambayoyin akwai karin bayani kan dalilan da suke haddasa dumamar yanayi ko tsananin zafi a sassan duniya.

 • Karin bayani kan kasar da aka fara yiwa mulkin mallaka a nahiyar Afrika
  Karin bayani kan kasar da aka fara yiwa mulkin mallaka a nahiyar Afrika
  Duración: 20min | 11/08/2018

  Shirin Tambaya da Amsa na wannan makon ya amsa wasu daga cikin tambayoyin da masu sauraro suka nemi a yi musu karin haske akai, daga ciki akwai karin bayani kan yanki ko kasar da aka fara yiwa mulkin mallaka a tarihi.

 • Tarihin Hajiya Rabi Tambara uwar marayu a Nijar
  Tarihin Hajiya Rabi Tambara uwar marayu a Nijar
  Duración: 20h04min | 04/08/2018

  Shirin tambaya da amsa na wannan mako zai mayar da hankali zuwa tambayar daya daga cikin masu sauraren mu dangane da rayuwar Hajiya Rabi Tambara uwar marayu dake yar Majalisa a Nijar. Shirin amsa da tambaya tareda Shamsiya Hamza Ibrahim,wacce ta kuma duba wasu daga cikin tambayoyin masu saurare.

 • Karin bayani akan bakan gizo da kuma abinda ya kunsa
  Karin bayani akan bakan gizo da kuma abinda ya kunsa
  Duración: 20h03min | 28/07/2018

  Shirin Tambaya da Amsa na wannan lokaci, kamar yadda aka saba, ya tuntubi masana ko kuma kwararru kan wasu daga cikin tambayoyin da masu sauraro suke neman karin bayani akai. Daga cikin tambayoyin akwai karin bayani akan bakan gizo, da kuma gaskiyar ko yakan shanye ruwan sama idan hadari ya hadu.

 • Hasken wayar hannu na haifar da illa ga lafiyar Idanu
  Hasken wayar hannu na haifar da illa ga lafiyar Idanu
  Duración: 19min | 21/07/2018

  Shirin Tambaya da amsa, ya yi karin bayani kan matakan da ya kamata masu amfani da wayar hannu su dauka, wajen karewa ko rage illar da hasken wayoyi ko Komfuta ke haifarwa ga Idanu. Shirin ya kuma amsa wasu tambayoyin da masu sauraro suka nemi da a amsa musu.

 • Dalilan da suka haddasa yakin duniya na 1 da na 2
  Dalilan da suka haddasa yakin duniya na 1 da na 2
  Duración: 19min | 14/07/2018

  Shirin Tambayoyinku da Amsa na wannan mako, yayi karin haske ne akan dalilan da suka haddasa yakin duniya na farko da na daya, da kuma dalilan da zasu haddasa yakin duniya na uku da ake hasashen zai auku a nan gaba. Shirin ya kuma amsawa masu sauraro wasu karin tambayoyin da suka aiko masa.

 • Hanyoyin da ake bi wajen buga takardar kudin kasashe
  Hanyoyin da ake bi wajen buga takardar kudin kasashe
  Duración: 18min | 07/07/2018

  A cikin shirin tambayoyin ku masu saurare,tambayoyi dangane da hanyoyin da ake bi wajen buga takardun kudin kasashen Duniya,da tarihin Fela wanda ya sha'ara a duniyar mawakan Najeriya. Banda haka akwai tambayoyi da suka shafi Duniyar kwallon kafa dake gudane a Rasha. Tambaya da amsa daga sashen hausa na rediyon Faransa Rfi.

 • Amsa kan dalilan da ke haddasa aman wutar dutse da grgizar kasa
  Amsa kan dalilan da ke haddasa aman wutar dutse da grgizar kasa
  Duración: 19h06min | 30/06/2018

  Shirin tambaya da amsa tare da Shamsiyya Hamza Ibrahim ya amsa tambayoyin da ke bayani kan dalilan da ke haddasa girgizar kasa da aman wutar Dutse dama tambaya kan yadda ake yiwa shugabanni kiranye idan sun gaza aikata abin da aka zabe don yi. A yi saurare lafiya.

 • Ko kun san kasar da tafi yawan adadin mata a duniya?
  Ko kun san kasar da tafi yawan adadin mata a duniya?
  Duración: 20h00s | 02/06/2018

  Shirin Tambaya da Amsa na wannan mako, ya tattauna da masana ne akan tambayoyin da suka hada da neman sanin kasar da ke kan gaba wajen yawan adadin mata a duniya. Sai kuma karin bayani akan neman sanin menene kimiya. Shirin ya kuma karkare da bayani akan wasu tambayoyin da masu sauraro suka aiko akan Azumi.

 • Tambaya dangane da rayuwa cikin Sahara
  Tambaya dangane da rayuwa cikin Sahara
  Duración: 20min | 26/05/2018

  A cikin shirin tambayoyin ku masu saurare,Faruk Yabo ya samu wasu daga cikin amsoshin tambayoyin ku,musaman rayuwa cikin Sahara,dama ta yadda ya kamata a gudanar da azumin ramadana. Banda haka ya jiyo ta bakin masana dangane da kimiya.

 • Tarihin Marigayi Shiekh Isyaka Rabiu
  Tarihin Marigayi Shiekh Isyaka Rabi'u
  Duración: 20h05min | 12/05/2018

  Shirin Tambaya da Amsa na wannan makon yayi karin bayani akan Tarihin marigayi Shiekh Isayaka Rabi'u, shugaban darikar Tijjaniya ta nahiyar Afrika. Zalika shirin yayi karin haske akan tambayar da aka nemi sanin doka da kuma yadda ake kafa dokoki.

 • Amsoshin tambayoyin ku daga Dr Meddy
  Amsoshin tambayoyin ku daga Dr Meddy
  Duración: 19min | 05/05/2018

  A cikin shirin amsoshin ku masu saurare,Dr Meddy mai zane-zanen shagube ya amsa wasu daga cikin tambayoyin ku  tareda duba wasu daga cikin manufofin kamar yadda masu saurare suka bukaci ji daga gare shi. Faruk Yabo ne ya jagoranci shirin tareda hadin gwiwar abokanin aiki daga sashen hausa da Swahili a Tanzania.

 • Matsayin sandar da ake ajiyewa a Majalisa yayin kafa dokoki
  Matsayin sandar da ake ajiyewa a Majalisa yayin kafa dokoki
  Duración: 20min | 28/04/2018

  Shirin Tambaya Da Amsa na wannan makon yayi karin haske akan tambayoyin da suka hada da neman sanin muhimmancin kasancewar sanda a majalisar tarayyar Najeriya, sai kuma neman sanin tarihin masarautar Gwandu da ke Najeriya.

 • Rashin barci kan iya janyowa dan Adam cutar hauka
  Rashin barci kan iya janyowa dan Adam cutar hauka
  Duración: 18min | 21/04/2018

  A cikin shirin tambaya da amsa, Faruk Yabo ya jiyo ta bakin likita ko rashin barci kan iya  janyowa dan Adam cutar hauka, banda haka  ya kuma kawo amsoshi ga wasu daga cikin tambayoyin ku masu saurare.

 • Wasa tsakanin wasu kabilu a Duniyar Hausa
  Wasa tsakanin wasu kabilu a Duniyar Hausa
  Duración: 20h01min | 14/04/2018

  A cikin shirin tambaya da amsa, da ke mai da hankali ga wasu daga cikin tambayoyin ku masu sauraren gidan rediyon Faransa Rfi, Faruk Yabo ya tabo wasu daga cikin tambayoyin ku musaman yadda wakilan gidajen rediyo ke harhadawa, tacewa kazalika da aike da rahotanni. shirin har ila yau, ya duba asalin wasa tsakanin Kanawa da zazzagawa.

 • Tarihin dan Tauri a yankin hausa
  Tarihin dan Tauri a yankin hausa
  Duración: 19min | 07/04/2018

  A cikin shirin tambaya da amsa ,Abubakar Issa Dandago ya duba wasu daga cikin tambayoyin ku masu saurare da suka shafin rayuwar dan tauri a duniyar Hausa,ya kuma ji ta bakin wasu daga cikin masana al'adar hausa

 • Tarihin masanin kimiyya Stephen Hawking
  Tarihin masanin kimiyya Stephen Hawking
  Duración: 20h00s | 31/03/2018

  Shirin Tambaya da Amsa na wannan makon ya yi karin bayani ne akan Tarihin Shahararren masanin kimiyya na Duniya Stephen Hawking, tarihin tsohon dan Majalisar Dattijan Najeriya Marigayi Sanata Ali Wakili.

 • Tarihin gasar Europa
  Tarihin gasar Europa
  Duración: 20h02min | 24/03/2018

  Shirin Tambaya da Amsa na wannan makon ya yi gamsasshen bayani akan tarihin gasar kwallon kafar nahiyar turai ta Europa da kuma yawan kungiyoyin da suke buga ta. Zalika shirin ya amsa tambayoyin da suka shafi tarihi na Sarauta a kasar Hausa da kuma kan sha'anin Diflomasiyya tsakanin manyan kasashen duniya.

 • Karin bayani akan cutar kuturta da kuma yadda ake daukarta
  Karin bayani akan cutar kuturta da kuma yadda ake daukarta
  Duración: 19min | 10/03/2018

  Shirin 'Tambaya da Amsa' na wannan makon, ya yi karin haske ne akan tambayar da aka nemi karin haske akai, dangane da cutar kuturta da kuma yadda ake daukar ta. Shirin kuma ya amsa tambayoyi akan 'yan wasan kwallon kafa da suka fi daukar albashi, sai kuma tarihin kafuwar kungiyar kwadago ta Najeriya.

 • Tarihin Daular Borno da karin bayani kan yawan Sarakunanta
  Tarihin Daular Borno da karin bayani kan yawan Sarakunanta
  Duración: 19min | 24/02/2018

  Shirin Tambaya da Amsa na wannan makon, ya yi karin bayani kan tarihin masarautar Borno da tsirin mulkinta a nahiyar Afrika, da kuma yawan sarakunan da suka jagorance ta. Kamar yadda aka saba kuma shirin ya amsa wasu karin tambayoyin da masu sauraro suka aiko, ciki har da tarihin jihar Kano.

 • Yawan kasashen Africa renon kasar Faransa
  Yawan kasashen Africa renon kasar Faransa
  Duración: 19min | 17/02/2018

  Cikin wannan shiri na Tambaya da Amsa da Azima Bashir Aminu ke gabatarwa za'a ji amsa game da yawan kasashen Africa da Faransa ta yi masu mulkin mallaka, Akwai kuma bayani dangane da cutar kusumbi.

 • Karin bayani kan dalilan da suke haddasa goyon ciki a bayan mahaifa ga mace
  Karin bayani kan dalilan da suke haddasa goyon ciki a bayan mahaifa ga mace
  Duración: 19min | 10/02/2018

  Shirin na wannan mako kamar yadda aka saba ya amsa wasu daga cikin tambayoyin da kuka nemi karin bayani akansu. Daga ciki akwai neman karin bayani kan dalilan da suke haddasa juna biyu ya zauna a wajen Mahaifa. Zalika shirin ya yi karin bayani akan ayyukan kungiyar Al Shebaab.

 • Karin bayani kan wasan kwallon kafa na El-Classico tsakanin Real Madrid da Barcelona
  Karin bayani kan wasan kwallon kafa na El-Classico tsakanin Real Madrid da Barcelona
  Duración: 19min | 03/02/2018

  Shirin Tambaya da Amsa na wannan makon, ya yi karin bayani kan wani bangare na tarihin wasan kwallon kafa tsakanin kungiyar Real Madrid da kuma Barcelona, wanda ake yi wa taken El Classico. Shirin, ya kuma amsa wasu tambayoyin da ku masu sauraro kuka aiko dan neman karin bayani, daga ciki kuma akwai neman tarihin Dutsen Tanguma na kabilar Arawa a Jamhuriyar Nijar.

 • TAMBAYA DA AMSA-Karin bayani kan maadanan kasa
  TAMBAYA DA AMSA-Karin bayani kan ma'adanan kasa
  Duración: 20h05min | 27/01/2018

  Shirin Tambaya da amsa ya nemi karin bayani daga masana, akan tarihin kalandar miladiyya da masu sauraro suka nemi sani. Zalika kamar yadda aka saba, shirin ya masa wasu tambayoyin da ku masu sauraro ke aikowa domin neman karin bayani.

 • Tarihin yadda aka samo kalandar miladiyya
  Tarihin yadda aka samo kalandar miladiyya
  Duración: 19min | 13/01/2018

  Shirin Tambaya da amsa ya nemi karin bayani daga masana, akan tarihin kalandar miladiyya da masu sauraro suka nemi sani. Zalika kamar yadda aka saba, shirin ya masa wasu tambayoyin da ku masu sauraro ke aikowa domin neman karin bayani.

 • Darajar kudin Bitcoin
  Darajar kudin Bitcoin
  Duración: 19min | 06/01/2018

  A cikin shirin  za mu kawo maku wasu daga cikin amsoshin da suka shafi  tattalin arziki kama daga Bitcoin. Akwai wasu tambayoyin da muka mika zuwa  mutanen da suka dace.

 • Tarihin jihar Kaduna dake tarrayar Najeriya
  Tarihin jihar Kaduna dake tarrayar Najeriya
  Duración: 19min | 30/12/2017

  A cikin shirin amshoshin masu saurare Azima Aminu ta jiyo ta bakin masana tarihi kan kafuwar Jihar Kaduna . Ta kuma samo wasu daga cikin amsoshin masu saurare rfi a cikin shirin.

 • Tarihin akwatin rediyo
  Tarihin akwatin rediyo
  Duración: 19min | 09/12/2017

  A cikin shirin amsoshin masu saurare,Azima Aminu ta yi kokarin samo amsar tambayar tarihin akwatin Rediyo da wasu tambayoyin can daban.   sai ku biyo mu.....

 • Tarihi da karin haske kan yanayin siyasar kasar Iran
  Tarihi da karin haske kan yanayin siyasar kasar Iran
  Duración: 20min | 02/12/2017

  Shirin Tambaya da Amsa na wannan makon ya yi karin haske ne kan Tarihi da kuma salon siyasar kasar Iran. Zalika shirin ya amsa tambayar masu sauraro kan tarihin tsohon shahararren dan wasan kwallon kafa na kasar Liberia kuma dan takarar shugabancin kasar wato George Weah.

 • Karin bayani kan asali ko tushen harshe
  Karin bayani kan asali ko tushen harshe
  Duración: 19min | 25/11/2017

  Shirin na wannan mako ya yi karin haske kan tambayoyin da masu sauraro suka nemi karin haske a kai, daga ciki akwai karin bayani kan asali ko kuma tushen harshe, sai kuma neman sanin amfanin wakan jego ga macen da ta haihu.

 • Tarihin Kungiyar Al Shebab
  Tarihin Kungiyar Al Shebab
  Duración: 19min | 04/11/2017

  Kungiyar Al Shebab na Somalia  na daya daga cikin kungiyoyin dake  barazana ga batun tsaroa  akasar Somalai   da wasu kasashen ketare. A cikin shirin amsoshin masu saurare Azima Aminu  Bashir ta duba tambayar wani mai sauraren mu ,ga kuma shirin amsoshin tambayoyin ku masu saurare.

 • Tarihin kungiyar al Shebaab da dalilan da ya sa suka addabi Somalia
  Tarihin kungiyar al Shebaab da dalilan da ya sa suka addabi Somalia
  Duración: 19min | 28/10/2017

  Shirin Tambaya da Amsa na wannan yayi karin haske kan bukatar samun tarihin Kungiyar Al Shebaab mai da'awar Jihadi a kasar Somalia, da kuma dalilian da suka sanya har yanzu aka kasa kawo karshensu. Zalika shirin na dauke da amsoshin wasu tambayoyin da masu sauraro suka turo.

 • Tarihin Kaigaman Adamawa, Farfesa Pate
  Tarihin Kaigaman Adamawa, Farfesa Pate
  Duración: 20min | 14/10/2017

  Shirin tambayoyi da amsa na wannan makon ya yi kokarin amsa tambayoyi da daban daban da muka samu daga masu saurarenmu, in da muka fara da tambayar da ke bukatar tarihin Kaigaman Adama, Farfesa Umar Pate. Kazalika shirin ya ci gaba da hira da gogeggen dan siyasar Nijar, wato Dr. Sanusi Tambari Jako.

 • Ci gaban tarihin Sanusi Tambari Jaku na Nijar
  Ci gaban tarihin Sanusi Tambari Jaku na Nijar
  Duración: 19min | 07/10/2017

  Shirin tambayoyi da amsa na wannan makon tare da Garba Aliyu Zaria ya amsa tambayoyin da masu saurare suka aiko, ciki har da tambayar da ta bukaci tarihin tsohon dan siyasa a Nijar, Dr. Sanusi Tambari Jaku.

 • Tarihin Dokta Sanoussi Jackou daga Jamhuriyar Nijar
  Tarihin Dokta Sanoussi Jackou daga Jamhuriyar Nijar
  Duración: 20h00s | 30/09/2017

  A cikin shirin tambaya da amsa daga sashen hausa na rediyon Faransa RFI,masu saurare sun bukaci Garba Aliyu ya  kawo masu tarihin dan siyasar Nijar Dokta Sanoussi Tambari Jackou.  

 • Tarihin Tsibiri a ckin shirin amshoshin tambayoyin masu saurare
  Tarihin Tsibiri a ckin shirin amshoshin tambayoyin masu saurare
  Duración: 19min | 23/09/2017

  A cikin shirin tambayoyin ku masu sauraren sashen hausa na gidan rediyon Faransa Rfi ,za ku ji ko a ina aka kwana dangane da batun  masarautar Tsibiri dake Jamhuriyar Nijar dama wasu amsoshin tambayoyin ku a kai.      

 • Karin bayani kan alakar sauyin yanayi da kuma guguwa da ke tasowa daga teku
  Karin bayani kan alakar sauyin yanayi da kuma guguwa da ke tasowa daga teku
  Duración: 20min | 17/09/2017

  Daya daga cikin batutuwan da shirin Tambayoyinku da Amsa na wannan makon yayi karin haske a kai shi ne; Alakar canjin yanayi da aukuwar guguwa, kashe-kashenta da kuma yadda guguwar ke tasowa daga teku.

 • Tarihin masarautar Kanem Borno da alakarta da sauran masarautu
  Tarihin masarautar Kanem Borno da alakarta da sauran masarautu
  Duración: 17min | 03/09/2017

  Shirin Tambaya da Amsa wanda a makonnan Salisou Hamisou ya gabatar, ya amsa tambayar da ku masu sauraro kuka gabatar, ta neman karin bayani kan masarautar Kanem Borno da kuma alakarta da sauran masarautun waccan lokacin da ke ciki da wajen Najeriya. Sai kuma sauran tambayoyin da shirin ya amsa kan wasu fannonin daban.

 • Shiek Abdullahi Uwais: Karin haske kan alamuran da suka shafi Layya
  Shiek Abdullahi Uwais: Karin haske kan al'amuran da suka shafi Layya
  Duración: 20min | 26/08/2017

  Shirin Tambaya da Amsa na wannan mako da AbduRahman Gambo Ahmad ya gabatar, ya yi karin haske ne kan tambayoyin da masu sauraro suka aiko kan neman karin bayani bisa al'amuran da suka shafi Ibadar Layya, Lafiya (bayani kan ciwon Basir), sai kuma rikicin yankin gabas ta tsakiya.

 • Hanyoyin warkar da cutar kuturta
  Hanyoyin warkar da cutar kuturta
  Duración: 20min | 19/08/2017

  A cikin shirin  amsoshin tambayoyin masu saurare,mu ji ta bakin likita  dangane da cutar kuturta dama hanyoyin warkar da ita.    

 • Amfanin cin namijin Goro
  Amfanin cin namijin Goro
  Duración: 19min | 12/08/2017

  A cikin shirin tambaya da amsa ,Abdurahamane Gambo ya samu zantawa da masana dangane da wasu daga cikin tambayoyin ku,kamar wannan tambaya ko mai nene amfanin cin namijin goro,ga dai amsar a cikin shirin amsoshin ku masu saurare.  

 • Tarihin Shahararren Magini Na Kasar Hausa Muhammadu Durugu wanda aka fi sani da Babban Gwani
  Tarihin Shahararren Magini Na Kasar Hausa Muhammadu Durugu wanda aka fi sani da Babban Gwani
  Duración: 20min | 05/08/2017

  Cikin wannan shiri za'a ji tarihin wani shahararren magini Muhammadu Durugu wanda aka fi sani da Babban Gwani a kasar Hausa. Akwai kuma amsar tambaya game da gandun daji na Bauchi dake Arewacin Najeriya.

 • Kamfanin dilancin labaran Faransa na Afp ,mai nene sahihancin kamfanin
  Kamfanin dilancin labaran Faransa na Afp ,mai nene sahihancin kamfanin
  Duración: 19min | 15/07/2017

  Kamfanin dilancin labaran Faransa na AFP ya fara aiki  a shekara ta 1944, cibiyar kamfanin na Paris a kasar Faransa. a ckin shirin amshoshin masu saurare za ku ji karin haske  a kai.    

 • Rayuwar Marigayi Dan Masanin Kano Yusuf Maitama Sule
  Rayuwar Marigayi Dan Masanin Kano Yusuf Maitama Sule
  Duración: 19min | 08/07/2017

  Shirin ya amsa tambayoyin da masu saurare suka aiko inda suka nemi bayani akan rayuwar Marigayi Alhaji Yusuf Maitama Sule Dan Masanin Kano da Allah Ya yi wa rasuwa. Shirin ya tattauna da abokinsa kuma amininsa Galadiman Katsina Mai tsohon Alkalin Alkalan Najeriya mai Shari'a Mamman Nasir. Sannan akwai tambaya akan asalin Aula Sarkin dubara.

 • Bambancin Turancin Ingila da na Amurka
  Bambancin Turancin Ingila da na Amurka
  Duración: 20h00s | 01/07/2017

  Shirin ya yi kokarin amsa tambayoyi da suka shafi banbancin da ke tsakanin Turancin Ingila da na Amurka da kuma tambaya akan lafiyar dabbobi, ta yadda cuta ke yaduwa a tsakaninsu.

Informações: