Ilimi Hasken Rayuwa

Tasirin fasahar AI da ke aron basirar dan Adam ga na'urori a fannin Ilimi

Informações:

Sinopsis

Shirin wannan mako dai ya yi nazari ne kan fasahar nan ta na'urar da ake sanya wa tunanin dan adam wato Artificial Intelligence, wadda a yanzu hankalin kasashen duniya ya fi karkata akai ganin yadda ya zo da gagarumin sauyi mai ban mamaki.   Sai dai duk da ci gaban da wannan fasahar ta zo da shi da ma wanda ake hasashen za ta samar nan da shekaru kadan masu zuwa, hankalin kasashen duniya ya rabu gida biyu wurin ci gaba da amincewa da wannan fasaha.