Ilimi Hasken Rayuwa

Informações:

Sinopsis

Wannan Shirin ya shafi Fadakar da al'umma game da ci gaban da aka samu a sha'anin Ilimi a fannoni daban-dabam a duniya, tare da nazari ga irin ci gaban da aka cim ma wajen binciken kimiya da fasaha da ke naman saukakawa Danadam wajen tafiyar da rayuwarsa a duniya. Shirin kuma zai yi kokarin jin irin bincike da masana ke yi domin inganta rayuwar Biladam. Shirin na zo maku ne, a duk ranar Talata a shirye-shiryenmu na safe.

Episodios

  • An samar da cibiyar sadarwa a jahar Bauchi don saukakawa dalibai wajen bincike

    19/03/2024 Duración: 09min

    Shirin Ilimi Hasken Rayuwa a wannan lokacin ya yi duba ne kan yadda wasu kungiyoyi karkashin cibiyar fasahar sadarwa da ci gaban al’umma wato CITAD suka samar da wata katafariyar cibiyar sadarwa da aka yiwa lakabi da HELLO HOPE a jahar Bauchi. Shirin ya kasance wani bangare na yunkurin saukakawa mazauna karkara hanyoyin samun sadarwa ta internet musamman wuraren da babu irin wannan ci gaba ko kuma wuraren da suke da shi amma bashi da karfi, wanda jama’are ke cikin wannan rukuni. Kungiyoyin da sun sha alwashin samar da irin wannan cibiyar sadarwa guda 20 a shiyoyin Najeriya shida zuwa karshen wannan shekara domin samar da internet a yankunan karkara.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna........

  • Taro kan gudummawar kafafen yada labarai a bangaren tsaro a jami'ar ABU Zaria

    05/03/2024 Duración: 09min

    Matsalar tsaro na daya daga cikin matsalolin da ke addabar Najeriya, musamman ma arewacin kasar, hakan ya  sanya sashen koyon aikin jarida na jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria da ke jihar Kaduna ya shirya wani taro gagarumin taro na kasa da kasa domin tattaunawa a kan gudumawar da kafafen yada labarai za su iya bayarwa wajen warware matsalar tsaro. Ya yi wannan ne da zummar taimaka wa kokarin da al'umma ke yi wajen warware wa kansu matsalar tsaron da ke damun su.

  • Yadda dalibai ke barin karatu a Nijar don tafiya neman kudi a wasu kasashe

    27/02/2024 Duración: 10min

    Shirin Ilimi Hasken Rayuwa a wannan lokacin ya yi duba ne kan yadda dalibai da dama a Jamhuriyar Nijar, musaman maza ke barin karatu da sunan tafiya neman kudi, kasashen ketare kamar Libiya, Aljeriya ko kuma hako zinare a kasar Mali kai harma da kokarin tsallakawa Turai, abin da ya sanya kungiyoyin dalibai a kasar bazama aikin wayar da kan matasa kan sanin muhimmancin da ilimi ke da shi. A Nijar kashi 25 na yara ne ke samun zuwa makarantar boko, kuma daga yara 100 da ake sanyawa a makarantun firamare uku kadai ke kaiwa matakin jami’a.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna........

  • Yadda gwamnatin jahar Neja ta fara horas da dalibai sana'oin dogaro da kai

    20/02/2024 Duración: 10min

    Shirin 'Ilimi Hasken Rayuwa' na wannan makon zai yi duba ne kan yadda gwamnatin jahar Neja da ke Arewacin Najeriya, ta samar da shirin horas da dalibai sana'oin hannu don dogaro da kai. Gwamnatin jahar dai ta ware ranar Juma'ar kowane mako don gudanar da darasin koyon sana'oin hannu. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna........

  • Yadda amfani da komfuta ya shafi kyaun rubutun dalibai

    31/01/2024 Duración: 09min

    A wannan makon zamu duba yadda ci gaban kimiyya da Ilimi ke zama wani nau’I na koma baya musamman a tsakanin dalibai a Najeriya.Tun bayan samar ko kuma kirkirar na’urar kwamfuta a 1837, da kuma shigowar ta Najeriya karon farko a 1963 sannu a hankali take bazuwa tsakanin jama’a, yayi da kuma ake samun ci gaba ta fannin amfani da ita. 

  • Gwamnatin Neja na shirin farfado da tsarin karatun makiyaya

    19/12/2023 Duración: 09min

    Shirin 'Ilimi Hasken Rayuwa' na wannan makon zai yi duba ne da tsarin karatun 'yayan makiyaya, wato Nomadic Education. Gwamnatin jihar Neja ce ta yi hobbasa don farfado da shirin karatun 'yayan makiyaya a jihar. Shirin zai bai wa makiyaya damar samun ilimi a duk inda suka yi balaguro don inganta makomarsu. Yanzu haka dai shirye-shirye sun yyi nisa a game dfdaa wannan shirin a jihar Neja  mai fara da matsalar tsaro sakamakon ayyukan 'yan bindiga da ke kashe mutane da satar su don kudin fansa.

  • Taimakon da kirkirarren Tabarau ke bai wa masu fama da matsalar raunin gani

    28/11/2023 Duración: 10min

    Shirin 'Ilimi Hasken Rayuwa' na wannan makon tare da Shamsiyya Haruna ya maida hankali ne kan nazarin da masana kimiya suka yi wajen kirkirar Tabaraun hangen nesa, don taimakawa masu raunin gani. A jamhuriyar Nijar, matsalar gani na zama babban kalubale ga al'ummar kasar wacce a yanzu har aka fara samunta a tsakanin matasa. Tuni dai matsalar ta sanya likitoci fara kiraye-kiraye ga al'umma da su tashi tsaye wajen kula da lafiyar idonsu.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin......

  • Iyayen dalibai a Nijar na kokawa kan tsadar kudin karatu

    14/11/2023 Duración: 10min

    Shirin 'Ilimi Hasken Rayuwa' na wannan makon tare da Shamsiyya Haruna ya maida hankali ne kan yadda iyaye ke kokawa a jamhuriyar Nijar kan tsadar kudin karatun 'ya'yansu, masamman makaruntu masu zaman kansu saboda matsaloli na tsadar rayuwa da aka shiga tun bayan da sojoji suka yi juyin mulki.

  • Najeriya: Yadda tsadar man fetur ke ci gaba da yin tasiri kan harkar ilimi

    31/10/2023 Duración: 10min

    Shirin 'Ilimi Hasken Rayuwa' na wannan mako tare da Shamsiyya Haruna ya maida hankali ne  kan yadda matsalar tsadar man fetur ke ci gaba da yin tasiri akan harkar ilimi a Najeriya, wanda tun bayan sanar da janye tallafin mai a kasar kanana da manyan makarantu ke daukan matakai daban daban da zummar daidaita harkokinsu a cikin wannan yanayi.  Daga cikin wadannan matakai, wasu manyan makarantun musamman jami'o'i sun takaita ranakun zuwan aikin malamai tare da tsawaita lokutan darrusan dalibai.

  • Yadda za'a karfafa ilimin fasaha a Najeriya

    24/10/2023 Duración: 10min

    Shirin ilimi hasken rayuwa na wannan mako ya duba taron fayyace zakakuran matasan da ke da fasahar zamani don karfafa musu gwiwa da fadada ilimin su. Danna alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna

  • Tsarin koyar da ilimin Computer ga daliban da ke shirin shiga jami'a a Nijar

    10/10/2023 Duración: 10min

    Shirin Ilimi hasken rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali kan tasirin ilimin fasahar na'ura mai kwakwalwa ko kuma computer ga daliban da ke shirin shiga jami'a a Jamhuriyyar Nijar, sabon tsarin da aka bijiro da shi da nufin taimakawa tarin daliban da basu da gogewa a fannin na fasahar na'urar computer. Wannan mataki dai na da nasaba da yadda ake samun tarin dalibai da basu da cikakkiyar gogewa a fannin na ilimin fasahar na'urar Computer, lamarin da ke zama tarnaki ga tsarin koyo da koyarwar zamani da komi ke shirin komawa tsarin amfani da na'urar ta computer.Ku latsa alamar sauti don saurarin cikakken shirin...................

  • Gudunmowar ilimin sararin samaniya ga ci gaban duniya

    12/09/2023 Duración: 10min

    Shirin Ilimi hasken rayuwa na wannan mako ya yi duba ne kan irin rawar da nazarin ilimin sararin samaniya ke bada gudunmowa wajen habbaka ci gaban duniya. Danna alamar saurare don jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna

  • Yadda dalibai ke gaza cin jarabawa ta komfuta

    15/08/2023 Duración: 10min

    Shirin 'Ilimi Hasken Rayuwa' na wannan mako ya yi duba ne da yada dalibai  ke faduwa a jarabawar da ake yi da na'urar komfuta, wato CBT exams. Dallibai dai na yawan kokawa a kaan yadda sukaa faduwa sosai a irin wannan jarabawa, sabanin wadda suka saba, ta alkalami da takarda. Hasali ma daliban naa gaanin cewa matsalar ba daga gare su take ba, inda suka kawo dalilai da dama da ke nnuna cewa ba su daa laifi don sun fadi irin wannan jarabawar.

  • Taron kungiyar malaman jaami'o'in shiyyar arewa maso yammacin Najeriya

    01/08/2023 Duración: 10min

    Shirin 'Ilimi Hasken Rayuwa' na wannan  makon ya mayar da hankali ne  kan taron kungiyar malaman jami'o'in shiyyar arewa maso yammacin Najeriya. Makasudin wannan taro kamar yadda kungiyar ta bayyana shine nazari kan irin ci gaban da aka samu ko akasinsa a jam'i'o'in shiyyar da zummar lalubo hanyoyin samun mafita.

  • Hanyoyin da ya kamata a bi wajen yaki da barayin waya a Najeriya

    11/07/2023 Duración: 09min

    Shirin ilimi hasken rayuwa na wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda masu satar waya suka addabi al'ummar jihar Kano, da ke arewacin Najeriya.

  • Yadda cire tallafin mai a ya shafi harkar ilimi a Najeriya

    27/06/2023 Duración: 09min

    Shirin 'Ilimi Hasken Rayuwa' ya yi nazarari ne kan cire tallafin mai da sabuwar gwamnatin Najeriya karkashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu ta yi, inda a lokacin da ya ke gabatar da jawabi jim kadan bayan rantsar da shi, Tinubu ya sanar da janye biyan kudin tallafin mai da gwamnatin kasar ke yi, lamarin da ya sa farashin makamashin ya yi tashin gwauron zabi, kuma ya haifar da karin matsin rayuwa a kasar musamman a  bangaren marasa karfi. Iyaye da daliban abin ya shafe su, ganin yadda matakin ya tilasta wasu iyaye fara tunanin sauyawa 'ya'yansu makaranta sabida kasa iya ci gaba da biyan kudin motar da ake kai su makaranta don neman ilimi, a dayan bangaren ma, al'amarin ya shafi su kansu malaman makartu tun daga matakin Firamari da Sakandari da ma manyan makarantu.Ku latsa alamar sauti donjin cikakken shirin..........

  • Tasirin fasahar AI da ke aron basirar dan Adam ga na'urori a fannin Ilimi

    14/06/2023 Duración: 10min

    Shirin wannan mako dai ya yi nazari ne kan fasahar nan ta na'urar da ake sanya wa tunanin dan adam wato Artificial Intelligence, wadda a yanzu hankalin kasashen duniya ya fi karkata akai ganin yadda ya zo da gagarumin sauyi mai ban mamaki.   Sai dai duk da ci gaban da wannan fasahar ta zo da shi da ma wanda ake hasashen za ta samar nan da shekaru kadan masu zuwa, hankalin kasashen duniya ya rabu gida biyu wurin ci gaba da amincewa da wannan fasaha. 

  • Tasirin tsarin koyarwa ta yanar gizo ko kuma E-Learning ga daliban Najeriya- 2

    06/06/2023 Duración: 10min

    Shirin Ilimi hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna na wannan mako ya ci gaba ne akan na makon jiya wanda ya mayar da hankali kan tasirin koyarwa ta yanar gizo ko kuma E-Learning, a Turance. 

  • Tasirin tsarin koyarwa ta yanar gizo ko kuma E-Learning ga daliban Najeriya

    30/05/2023 Duración: 09min

    Shirin Ilimi hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna ya mayar da hankali kan tsarin ilimi ta yanar gizo ko kuma na shafukan Intanet da ake kira da E-Learning ko kuma Digilal Learning. Tun bayan bullar cutar covid-19 ne dalibai da dama suka koma karatu ta yanar gizo ko kuma E-Learning a wani yunkuri na kaucewa ganin karatunsu bai gamu da tangarda ba.A cikin wannan shirin za ku ji tasirin irin wannan karatu da kuma tagomashin sa ga daliban Najeriya.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin...........

  • Ilimi Hasken Rayuwa, na magana kan halin da karatun yara yan gudun hijira ke ciki a Nijer

    23/05/2023 Duración: 10min

    A wannan makon Shamsiya Haruna ta duba yadda gwamnatin jamhuriyar Nijar ke kokari wajen samarwa yara yan gudun hijira guraban karatu a cikin makarantun bokon kasar gudun kar su yi biyu babu, ba gida ba kasa ba kuma Ilimi.

página 1 de 2