Ilimi Hasken Rayuwa

Informações:

Sinopsis

Wannan Shirin ya shafi Fadakar da al'umma game da ci gaban da aka samu a sha'anin Ilimi a fannoni daban-dabam a duniya, tare da nazari ga irin ci gaban da aka cim ma wajen binciken kimiya da fasaha da ke naman saukakawa Danadam wajen tafiyar da rayuwarsa a duniya. Shirin kuma zai yi kokarin jin irin bincike da masana ke yi domin inganta rayuwar Biladam. Shirin na zo maku ne, a duk ranar Talata a shirye-shiryenmu na safe.

Episodios

  • Ilimi Hasken Rayuwa, na magana kan halin da karatun yara yan gudun hijira ke ciki a Nijer

    23/05/2023 Duración: 10min

    A wannan makon Shamsiya Haruna ta duba yadda gwamnatin jamhuriyar Nijar ke kokari wajen samarwa yara yan gudun hijira guraban karatu a cikin makarantun bokon kasar gudun kar su yi biyu babu, ba gida ba kasa ba kuma Ilimi.

  • Karancin dakunan karatu na barazana ga karatun Firamare a Neja

    16/05/2023 Duración: 09min

    Shirin Ilimi hasken rayuwa tare da Shamsiyya Haruna ya mayar da hankali kan kalubalen da karatun Firamare ke fuskanta a jihar Neja ta tsakiyar Najeriya, dai dai lokacin da ake samu karuwar yaran da ke zuwa makaranta. Mahukuntan jihar Neja sun bayyana cewa adadin daliban da ke shiga Firamare a Neja ya karu daga yara dubu 600 zuwa dubu 800 a bana, sai dai matsalar karancin ajujuwa da kayakin karatun na matsayin babban koma baya ga bangaren ilimi na jihar.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin..............

  • Ko yaya makomar karatun daliban da aka kwashe daga Sudan take?

    09/05/2023 Duración: 10min

    Shirin na wannan rana, ya duba halin da karatun daliban da suke tsere daga Sudan ke ciki, yayin da rikici ya barke a kasar da ke gabashin Afirka. Najeriya na daga cikin kasashen da ssuka kwashe dalibai da kuma 'yan kasashen su da ke rayuwa a Sudan, yayin da aka wayi gari da karar harbin bindiga da kuma hare-hare ta sama.Kasar Sudan dai ta fada cikin rudani tun bayan da rikicin mulki ya barke tsakanin dakarun da ke biyayya ga babban hafsan soji Abdel Fattah al-Burhan da kuma tsohon mataimakinsa Mohamed Hamdan Daglo, wanda ke jagorantar rundunar kai daukin gaggaa ta Rapid Support Forces.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin da Shamsiyya Haruna ta gabatar.

  • Najeriya za ta fara kwashe daliban kasarta da ke Sudan zuwa Masar

    25/04/2023 Duración: 09min

    Hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya NEMA, ta ce sun fara tattaunawa da mahukuntan kasar Masar a birnin Alkahira, kan yadda za a kwaso daliban kasar daga Sudan, yayin da bangarori biyu ke ci gaba da gwabza yaki a kasar da ke Gabashin Afirka. Wannan ya zo ne, bayan da dubban dalibai 'yan Najeriyar da ke karatu a Sudan suka mika koken su ga gwamnatin kasar, game da mummunan yanayin da suke ciki, saboda tashe-tashen hankula a Khartoum, babban birnin ƙasar.Sojojin gwamnati da kuma dakarun RSF sun shafe sama da mako guda suna rikici da juna, lamarin da ya jefa fararen hula da dama cikin mummunan yanayi.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin da Shamsiyya Haruna ta gabatar.

página 2 de 2