Ilimi Hasken Rayuwa

Karancin dakunan karatu na barazana ga karatun Firamare a Neja

Informações:

Sinopsis

Shirin Ilimi hasken rayuwa tare da Shamsiyya Haruna ya mayar da hankali kan kalubalen da karatun Firamare ke fuskanta a jihar Neja ta tsakiyar Najeriya, dai dai lokacin da ake samu karuwar yaran da ke zuwa makaranta. Mahukuntan jihar Neja sun bayyana cewa adadin daliban da ke shiga Firamare a Neja ya karu daga yara dubu 600 zuwa dubu 800 a bana, sai dai matsalar karancin ajujuwa da kayakin karatun na matsayin babban koma baya ga bangaren ilimi na jihar.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin..............