Ilimi Hasken Rayuwa

Ko yaya makomar karatun daliban da aka kwashe daga Sudan take?

Informações:

Sinopsis

Shirin na wannan rana, ya duba halin da karatun daliban da suke tsere daga Sudan ke ciki, yayin da rikici ya barke a kasar da ke gabashin Afirka. Najeriya na daga cikin kasashen da ssuka kwashe dalibai da kuma 'yan kasashen su da ke rayuwa a Sudan, yayin da aka wayi gari da karar harbin bindiga da kuma hare-hare ta sama.Kasar Sudan dai ta fada cikin rudani tun bayan da rikicin mulki ya barke tsakanin dakarun da ke biyayya ga babban hafsan soji Abdel Fattah al-Burhan da kuma tsohon mataimakinsa Mohamed Hamdan Daglo, wanda ke jagorantar rundunar kai daukin gaggaa ta Rapid Support Forces.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin da Shamsiyya Haruna ta gabatar.