Bakonmu A Yau

  • Autor: Vários
  • Narrador: Vários
  • Editor: Podcast
  • Duración: 1:24:12
  • Mas informaciones

Informações:

Sinopsis

A kullum mukan gayyaci masana a fannoni daban daban domin tattauna wasu muhimman al'amurra da suka shafi kanun labarai a duniya. wani lokacin kuma wasu manyan jami'an gwamnati da masu fada aji sukan kawo muna ziyara domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin da suka shafe su ko kuma ci gaban kasa.

Episodios

  • Farfesa Bello Bada kan bullar sabuwar kungiyar ta'addanci a Najeriya

    08/11/2024 Duración: 03min

    Rundunar tsaron Najeriya ta tabbatar da samun wata sabuwar kungiyar 'yan ta'adda da ake kira Lakurawa a Jihohin Sokoto da Kebbi wadanda aka ce sun fito ne daga kasashen mali da Libya da kuma Jamhuriyar Nijar. Rahotanni sun ce 'yayan wanan kungiya na sanya haraji da kafa dokoki a yankunan da suke.Dangane da wannan sabon al'amari, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Bello Bada na Jami'ar Usman Dan Fodio dake Sokoto.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.

  • Sule Ammani kan abin da ya biyo bayan nasarar ƙubutar da yaran arewacin Najeriya

    06/11/2024 Duración: 03min

    Ga dukkan alamu matsalar da ta biyo bayan kama ƙananan yaran da ƴan sandan Najeriya su ka yi lokacin zanga-zangar tsaɗar rayuwa a Kano ta zaburar da wasu daga cikin shugabannin yankin kan bukatar haɗa kai domin ceto arewacin ƙasar daga halin da ya samu kansa, bayan sakin yaran, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da ɗaya daga cikin dattawan yankin Alhaji Sule Ammani Yarin Katsina.

  • Farfesa Shehu Abdullahi Zuru kan tasirin zaɓen Amurka ga Duniya

    05/11/2024 Duración: 03min

    Yau Amurkawa ke kaɗa ƙuri'a a zaɓen ƙasar da bayanai ke cewa fiye da mutum miliyan 180 za su jefa ƙuri'unsu don zaɓen guda cikin ƴan takara biyu da ke fafatawa wato tsohon shugaban ƙasar Donald Trump na jam'iyyar Republican da Kamala Harris ta Jam'iyyar Democrat wadda mataimakiyar shugaban ƙasa ce kuma ƴar takarar mace baƙar fata ta farko a tarihin ƙasar. Domin jin tasirin wannan zaɓe da ya ɗauki hankalin duniya Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Shehu Abdullahi Zuru na Jami'ar Baze.

página 2 de 2