Sinopsis
Muna gabatar muku da shirye-shirye masu ayatarwa da suka shafi al´adu da zamantakewa tsakanin al´ummomi da mabiya addinai daban-daban da nufin kyautata tsarin zamantakewa da fahimtar juna ta hanyar tuntuar juna da shawarwari tsakani ba tare da nuna fifiko akan wani ba.
Episodios
-
Taba Ka Lashe: 15.05.2024
21/05/2024 Duración: 09minShiri ne kan yadda kabilar Gwari ko Gbagi ke daukar kaya a kafada maimakon kai.
-
Taba ka Lashe 01.05.2024
01/05/2024 Duración: 09minShirin ya duba al'adar wasa tsakanin abokan wasa na jini wato dan mace da dan namiji da sauran wasanni da ke tsakanin hausawa da sauran kabilu.
-
-
Taba Ka Lashe: 10.4.2024
16/04/2024 Duración: 09minShirin Taba Ka Lshe game da kabilun da suka shiga kurmi daga sassan Najeriya da yarda suke samun cin karo da na kabilar Yarabawa.
-
Taba ka Lashe 21.03.2024
21/03/2024 Duración: 09minShirin ya duba yadda Bahaushe da masu mulkin mallaka suka sauya wa yankuna ya yi tasiri a bunkasar al'adun matunen yankunan da abin ya shafa a Kamaru.
-
Taba Ka Lashe: 14.02.2024
27/02/2024 Duración: 09minBikin taushen fage da dubban al’ummar garin Tsangaya da ke karamar hukumar Albasu a jihar Kano da ke Najeriya
-
Taba Ka Lashe: 21.02.2024
27/02/2024 Duración: 10minAl'ummar Jamhuriyar Nijar na ci gaba da jimamin rasuwar Alhaji Mahaman Kanta fitaccen dan Jarida kuma wakilin Deutsche Welle na farko a Jamhuriyar Nijar.
-
Taba Ka Lashe: 07.02.2024
13/02/2024 Duración: 09minKo kun san Kabilar Sayawa a jihar Bauchi da ke Najeriya, na da irin nata tsarin yadda take gudanar da bikin aure? Shirin Taba Ka Lashe
-
Taba Ka Lashe: 03.01.2024
03/01/2024 Duración: 09minShirin ya duba gasar karatun alkurani da aka shirya a jihar Yobe domin zabo gwarzaye da za su wakilci Najeriya a gasar duniya da ake yi, inda aka samu manyan baki da Sarkin Musulmin Najeriya.
-
Taba Ka Lashe: 27.12.2023
27/12/2023 Duración: 09minShirin ya duba bikin Hausa Kirista da aka saba gudanarwa a duk ranar 26 ga watan disambar kowace shekara sakamakon kirisimeti. Za mu ji yadda bikin ya samo asali a cikin bukukuwan al'adun Hausawa da ma yadda aka gudanar da shi.
-
-
Taba Ka Lashe: 15.11.2023
21/11/2023 Duración: 09minShin kun san tarihin Usman Baba Pategi wanda aka fi sani da Samanja mazan fama a shirin harkokin wasan kwaikwayo a arewacin Najeriya?
-
Taba Ka Lashe: 08.11.2023
13/11/2023 Duración: 09minKo kun san cewa marigayi Shehu Usman dan Fodiyo ya rubuta tarin litattafan ilimi, shirin Taba Ka Lashe na wannan lokaci ya yi nazari a kai.
-
Taba Ka Lashe: 25.10.2023
31/10/2023 Duración: 09minKabilar Dagomba guda ce daga cikin kabilun da ke da matukar tasiri a arewacin Ghana kuma ta yi biki nadi a birnin Kolon na Jamus.
-
-
Taba Ka Lashe: 04.10.2023
10/10/2023 Duración: 09minYadda al'umma a yankin Hausawa suke fadin sunayen yaransu na farko sabanin yadda aka sani a baya.
-
Taba Ka Lashe:26.09.2023
26/09/2023 Duración: 09minShirin ya duba muhimmancin tagwaye a lokacin aure a jihar Gaya ta Jamhuriyar Nijar, inda ake gayyatar 'yan biyu da ke a cikin gari da kewaye domin kawo gudurmuwa a wajen bikin 'yan biyu.
-
Taba Ka Lashe:19.09.2023
19/09/2023 Duración: 09minShirin ya nufi masarautar Abzinawa ta yankin Zinder da ke Jamhuriyar Nijar don duba tarihi da kuma al'adun masarautar har ma da irin rawar da take takawa wajen sasanta rikice-rikice tsakanin al'umma.
-
Taba Ka Lashe: (06.09.2023)
12/09/2023 Duración: 09minShirin na wannan lokaci, ya halarci bikin nunin fasahar zane-zane da fenti da rubuce-rubucen ayoyi ko surori da alamomi na tsayuwa ko wakafi ko kuma kowasula irinsa na farko da makarantar al-Kur'ani da take koyar da wannan darasi ta shirya a Kano.
-
Taba Ka Lashe: 24.08.2023
29/08/2023 Duración: 09minShirin ya duba yadda Mata 'yan kabilar Kanuri ke ci gaba da rike al'adar nan ta cire takalmansu domin girmama maza