Dandalin Fasahar Fina-finai

Informações:

Sinopsis

Fili ne na musamman kan Fina-finai ta hanyar tattauna da masu ruwa da tsaki a wannan fanni a duniya, Tare da wayar wa ma su sauraro kai da kara masu basira dangane da hikimar da Allah ya  bai wa wasu ta fanin shirya fim ko tsara wasan kwaikwayo. Wanda ke zo maku a duk ranar Asabar da safe, tare da maimaici a ranar Lahadi da yamma.

Episodios

  • Ko ana 'kan ta waye' a masana'antar Kannywood?

    06/02/2022 Duración: 20min

    Shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai' ya yi nazari ne a kan al'amarin nan da ake kira 'kan-ta-waye'. Shirin ya yi  bayani a kan menene 'kan-ta-waye', sannan ya tattauna da baki, wadanda suka fadada bayanin don fahimtar mai sauraro.

  • Rayuwar mata masu shirya fina-finai a Nollywood a Najeriya

    30/01/2022 Duración: 20min

    A cikin wannan shirin na dandalin fasahar Fina-finai,Hawa Kabir ta samun tattaunawa da masu ruwa da tsaki a Duniyar fina-finai dangane da makomar mata musaman a gidajen mazan su,ko wandada ke da niyar yin aure.

  • Halin da masana'antar Fim ta shiga a makon da ya kare

    09/01/2022 Duración: 20min

    Kamar yadda aka saba kowane mako shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai tare da Hauwa Kabeer ya tattauna akan wasu daga cikin muhimman al'amuran da ke wakana a masana'antar fina-fina da ke arewaci da kuma kudancin Najeriya.

  • Abinda ya wakana cikin kungiyar MOPAN a baya bayan nan

    19/12/2021 Duración: 20min

    Shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai' na wannan makon tare da Hauwa Kabeer, ya leka kungiyar MOPAN ne domin jin wainar da ake toyawa.

  • An kamala zaben wakilan kungiyar yan Fim a jihar Kaduna

    12/12/2021 Duración: 19min

    A cikin shirin duniyar fina-finai,Hawa Kabir ta samu tattaunawa da masu ruwa da tsaki a harakar fim yan lokuta bayan kamala zaben wakilan MOPAN a jihar Kaduna.Makomar duniyar Fim,hanyoyin kawo karshen baraka a wannan duniya na daga cikin manyan batutuwa da Hawa ta samu tattaunawa da bakin na ta.

  • Fitaccen makawaki ya sha alwashin daukar nauyin tallafawa mata da sana'o'i

    05/12/2021 Duración: 19min

    Shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai' na wannan makon tare da Hauwa Kabeer ya tattauna da wani fitaccen mawakin Hausa da ya sha alwashin daukar nauyin tallafawa mata da sana'o'i.

  • An fara daukar shirin 'Gidan Badamasi' zango na 4

    21/11/2021 Duración: 20min

    Shirin 'Dandalin Fasahar Fina Finai ya leka inda ake daukar shirin barkwancin nan mai dogon zango, wato 'Gidan Badamasi', inda ya gana da jarumai da masu ruwa da tsaki a shirin, cikin su har da babban daraktan shirin, Falalu Dorayi.

  • Rayuwar Alhaji Umaru Danjuma Katsina da aka fi sani da Kasagi

    07/11/2021 Duración: 20min

    Kasagi wanda ya rubuta fitaccen littafin da aka yi wa suna ‘Kulba na Barna’ ya rasu ne sakamakon gajeruwar rashin rashin lafiya.Danjuma Katsina na daya daga cikin fitattun masu wasan kwaikwayon da suka yi suna daga shekarar 1980 tare da wasu abokan aikin sa a lokacin irin su Kasimu Yero da Tumbuleke da Malam Mamman da karkuzu Na Bodara da kuma Samanja Mazan Fama. Hawa Kabir a cikin shirin dandalin fasahar fina-fanai ta jiyo ta bakin wasu daga cikin mutanen Danjuma Katsina wanda ke  daya daga cikin fitattun masu wasan kwaikwayon da suka yi suna daga shekarar 1980 tare da wasu abokan aikin sa a lokacin irin su Kasimu Yero da Tumbuleke da Malam Mamman da karkuzu Na Bodara da kuma Samanja Mazan Fama.Kasagi ya bada gudumawa sosai wajen daga darajar wasan kwaikwayo da ake sawa a wancan lokaci a Gidan Rediyo da talabijin Kaduna, yayin da littafin sa na ‘Kulba Na Barna’ ya shiga cikin jerin litattafan adabin da suka dauke hankalin dalibai da masu sha’awar karance karance na wancan lokaci.

  • Masu ruwa da tsaki kan rubutun adabi da fina-finai na alhinin rasa Kasagi

    31/10/2021 Duración: 20min

    Shirin Dandalin Fasahar Fina-Finai na wannan makon tare da Hauwa Kabir ya tattauna na masu ruwa da tsaki kan rubutun adabin Hausa da kuma fina finai kan rasuwar marigayi Umaru Danjuma Katsina da aka fi sani da Kasagi.

  • Taron kara wa juna sani kan habaka harshen Hausa 2/2

    24/10/2021 Duración: 20min

    Shirin 'Dandalin Fasahar Fina Finai tare da Hauwa Kabir ya cigaba da tattaunawa ne kan taron kara wa juna sani kan habaka harshen Hausa na kungiyar WTC da ya gudana a garin Zaria, dake jihar Kaduna.

  • Taron kara wa juna sani kan habaka harshen Hausa

    03/10/2021 Duración: 20min

    A cikin shirin 'Dandalin Fasahar Fina Finai, hauwa Kabir ta leka taron kara wa juna sani kan habaka harshen Hausa na kungiyar WTC  da ya gudana a Zaria, jihar Kaduna. Shirin ya gana da shehunan malaman da suka halarci taron. 

  • Rayuwar yan wasan fina-finai a Tarrayar Najeriya

    26/09/2021 Duración: 20min

    A cikin shirin dandalin Fina-finai,Hawa Kabir ta jiyo ta bakin  masu shirya fim a Nollywood,wanda suka kuma yi mata bayyana dangane da rayuwar su da kuma irin wasannin da suke iya kasancewa a cikin su ga baki daya.

  • Gudunmawar Ahmad Aliyu Tage ga masana'antar Kannywood

    19/09/2021 Duración: 20min

    Shirin dandalin Fasahar Fina-Finai na wannan makon ya tattauna kan rashin da masana'antar Kannywood tayi na wasu manyan jaruman ta, musamman Ahmad Aliyu Tage da ya rasu a makon da ya gabata.

  • Ta'aziyyar mawakin siyasa Isyaku Forest

    12/09/2021 Duración: 20min

    Shirin 'Dandalin Fasahar Fina Finai' na wannan mako tare da Hauwa Kabir ya kawo mana ta'aziyyar mawakin siyasan nan, Isyaku Forest, wanda ya rasu kwanan nan. Hauwa Kabir ta tattauna da makusanta da aminansa, ciki har da shahararren mawakin siyasa, Rarara.

  • Dalilan da suka haifar da koma baya ga kasuwar fina-finan Hausa

    05/09/2021 Duración: 20min

    Shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai' na wannan makon ya tattauna da masu ruwa da tsaki kan dalilan da suka janyo faduwar kasuwa fina-finan Hausa.

  • Mutane na yi wa fim kallon hadarin kaji don ba su ke yi ba - Isa Bello Ja

    29/08/2021 Duración: 20min

    A cikin shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai' Hauwa kabir ta kawo abubuwa da dama a bangaren fina-finai, inda ta duba yadda yanzu masana'antar Kannywood ke gogayya da takwararta tav kudancin Najeriya. Ta kuma tattauna da shugaban jaruman Kannywood, Alhassan Kwale wanda ya ce Umma Shehu da Sadiya Haruna ba 'yan Kannywood bane.

  • Tattaunawa da Yaya Dankwambo na shirin gidan Badamasi

    22/08/2021 Duración: 20min

    Shirin Dandalin Fasahar Fina-Finai na wannan makon tare da Hauwa Kabeer ya tattauna da Muhammadu Nura Yakubu da a yanzu aka fi sani da sunan Yaya Dankwambo na shirin fim din Gidan Badamasi.

  • Tattaunawa da Tijjani Asase (Damisa) kan masana'antar Kannywood

    15/08/2021 Duración: 20min

    Shirin Dandalin Fasahar Fina Finai ya tattauna da Tijjani Asase da aka fi sani da Damisa kan lamurran da suka shafi masana'antar Kannywood.

  • Ana shirin ci gaban fim din Hausa na 'Malam Zalimu'

    25/07/2021 Duración: 20min

    A cikin shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai' Hauwa Kabir ta duba tattauna da Ado Ahmed Gidan Dabino a game da ci gaban shirin fim din Malam Zalimu. Bayan nan ta leka Nollywood ta kudancin Najeriya, inda ta kawo ta'aziyar rasuwar shahararren mawaki, Sound Sultan.

  • Masu shirya Fina finan Hausa sun koma cin moriyar Youtube

    18/07/2021 Duración: 20min

    A cikin shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai' Hauwa Kabir ta yi dubi da batun kasuwanci a masana'antar Kannywood, tare da duba yadda masu shirya fim din suka koma intanet, ta wajen cin moriyar dandalin Youtube, inda suke dora ayyukansu a kai.

página 1 de 2