Bakonmu A Yau

Informações:

Sinopsis

A kullum mukan gayyaci masana a fannoni daban daban domin tattauna wasu muhimman al'amurra da suka shafi kanun labarai a duniya. wani lokacin kuma wasu manyan jami'an gwamnati da masu fada aji sukan kawo muna ziyara domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin da suka shafe su ko kuma ci gaban kasa.

Episodios

  • Arewa maso Yammacin Najeriya ne mafi hatsari saboda matsalar tsaro - Bincike

    18/04/2024 Duración: 03min

    Kungiyar 'Global Rights' ta bayyana yankin arewa maso yammacin Najeriya a matsayin mafi hadari, saboda yadda 'yan bindiga ke kisa da take hakkin Bil Adama ba tare da kaukautawa ba. Kungiyar tace a cikin shekaru 10 da suka gabata, yankin ya gamu da mummanar ukuba, fiye da sauran sassan Najeriya.Bashir Ibrahim Idris ya tintibi Dr Murtala Ahmad Rufai na Jami'ar Usman Danfodio, mawallafin 'I am a Bandit' kuma mai bincike a kan matsalar tsaron yankin.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.

  • Kuskure ne a yi tunanin ɗagawar darajar naira ba zai ɗore ba - Dakta Kurfi

    17/04/2024 Duración: 03min

    Darajar Naira na cigaba da ɗagawa a Najeriya tare da saukar farashin wasu kayayyakin abinci a wasu kasuwannin ƙasar, abinda ya sa wasu tunanin cewar tasirin saukar Dalar ne ya sanya wasu kayayyakin suka fara sauka. Wane hasashe masana tattalin arziƙi ke yi game da ci gaba da ɗagawar darajar Nairar, tare da zubewar Dala? Tambayar kenan da Abdulkadir Haladu Kiyawa, ya yi wa Dakta Ƙasim Garba Kurfi masanin tattalin arziki a Najeriya yayin tattaunawarsu.

  • Tattaunawa da Sanata Ikira Aliyu Bilbis kan tsaro a jihar Zamfara

    16/04/2024 Duración: 03min

    Hukumomi a Najeriya daga matakin jiha zuwa na kasar baki ɗaya na daukar matakai daban daban wajen samar da zaman lafiya a jihar Zamfara, amma har ya zuwa wannan lokaci ba'a kai ga cimma biyan bukata ba. Ɗan majalisar dattawan da ke wakiltar Zamfara ta Tsakiya, Ikra Aliyu Bilbis ya ziyarci ofishinmu dake Lagos, inda Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da shi akan halin da ake ciki.

  • Yadda rayuwa ta kasance bayan da muka faɗa hannun mayakan Boko Haram - Maryama

    15/04/2024 Duración: 03min

    A ranar Lahadi, 14 ga watan Afrilun nan aka cika shekaru 10 da sace dalibai mata na makarantar sakandaren Chibok sama da 250 da mayakan Boko Haram suka yi a jihar Borno. Bayan shafe wannan tsawon lokkaci dai har ya zuwa yau ba a iya gano wasu daga cikinsu ba.Ɗaya daga cikin daliban da suka kuɓuta mai suna Maryama, ta shaidawa Bashir Ibrahim Idris irin abubuwan da suka faru, daga lokacin da aka sace su da kuma lokacin da ta kuɓuta bayan shekaru 3.

  • Kwamred Bello Basi kan shirin gina hanyayoin zamani a Najeriya

    12/04/2024 Duración: 03min

    Gwamnatin Najeriya ta sanar da kashe naira biliyan 4 kan kowacce kilomita ta hanyar zamani da ake ginawa daga jihar Legas zuwa birnin Kalaba. Gwamnatin ta ce da zarar an kammala aikin za’a samar da shingen karbar kudade guda 50 da za’a rika karbar naira dubu uku kowanne ma’ana zuwa da dawowa mai karamar mota zai rike naira dubu 300, yayin da mai babbar mota da zai rika biyan naira dubu 5 zai rike naira dubu 500 a zuwa da dawowa.An dai yi zargin cewa gwamnatin ta yi amfani da sanayya ne wajen baiwa wani makusancin shugaban kasa wannan kwangila ba tare da bin ka’idojin da suka kamata ba.Kan wannan batu ne, Rukayya Abba Kabara, ta tattauna da Kwamred Bello Basi.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.

  • Farfesa Muntaqa Usman kan matakin korar ma'aikata da bankin CBN ya yi

    11/04/2024 Duración: 03min

    Babban Bankin Najeriya CBN na ci gaba da korar wasu daga cikin ma'aikatansa, inda a cikin kwanaki 20 da suka gabata bankin ya sallami ma'aikata 117 akasarinsu manyan ma'aikata. Kan haka Bashir Ibrahim Idris ya zanta da Farfesa Muntaqa Usman, masanin tattalin arziki a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar zantawar tasu.......

  • Tattaunawa da Imam Hussien bin Hycinth kan kyautata mu'amala bayan Ramadan

    10/04/2024 Duración: 03min

    Yau al'ummar Musulmin Najeriya suka bi sahun takwarorinsu na duniya wajen gudanar da Sallar Eid el Fitr. Limamin Jami'ar Lagos, Imam Isma'il Musa ya yi kira ga 'yan Najeriya da su kasance cikin masu hakuri daga halin da suka samu kansu kamar yadda addini ya faɗakar.Bayan kammala hudubar, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Imam Hussein bin Hycinth, kuma ga yadda zantawar su ta gudana.

  • Farfesa Mansur Isa kan darussan da ke cikin watan Azumin Ramadan

    09/04/2024 Duración: 03min

    Yau Musulmin duniya ke cika kwanaki 30 da fara azumin watan Ramadana, yayin da ake shirin bukukuwan Sallar Eid el Fitr daga gobe Laraba. Azumin na dauke da darussa da dama da Musulmi ke dauka.Ibrahim Malam Goje ya tambayi Farfesa Mansur Isa Yelwa na Jami'ar Abubakar tafawa Balewa dake jihar Bauchi a arewacin Najeriya, dangane da darussan da ya kamata musulmi ya yi amfani da su.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.

  • Baba Sheikh kan matakin yi wa mayakan Boko Haram afuwa da gwamna Zulum ya yi

    08/04/2024 Duración: 03min

    Gwamnatin Jihar Barno da ke Najeriya ta ce akalla mayakan Boko Haram sama da dubu 200 suka rungumi shirin ta na afuwa, inda suka aje makaman su da kuma mika kai domin horar da su da kuma sake musu tunani, kafain mayar da su cikin al'umma. Gwamnan jihar Babagana Umara Zulum ne ya kaddamar da shirin domin bai wa masu bukatar aje makaman su dama. Bashir Ibrahim Idris ya zanta da Baba Sheikh, mai magana da yawun gwamnan kan wannan batu.Ku latsa alamar sauti don sauraron yadda zantawarsu ta gudana.......

  • Abba Terab kan cire tallafin lantarki a Najeriya

    05/04/2024 Duración: 03min

    Hukumar Kula da wutar lantarki a Najeriya ta sanar da cire tallafin da gwamnati ke zubawa a bangaren samar da wutar ga wasu mutane, abinda ya shafi farashin wutar. Tuni jama’a da kungiyoyin kwadago da kuma masu masana’antu suka bara dangane da matakin da kuma abinda suka kira illar dake iya biyo baya.Malam Abba Terab, babban jami’i a hukumar ya yiwa Bashir Ibrahim Idris bayanin matakin da aka dauka a tattaunawar da suka yi a kai.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.

  • Dr Abdullahi Gwandu kan fara fitar da tatatcen mai, na matar man Dangote

    04/04/2024 Duración: 03min

    Matatar man hamshakin attajirin Najeriya Aliko Dangote ta fara fitar da albarkatun man fetur din da ta tace, kamar yadda daya daga cikin manyan jami’an kula da matatar da kuma kungiyar dillalan man fetur din a Najeriya suka tabbatar. A cewar jami’in, ya ce tuni suka fara rarraba wa ‘yan kasuwa man disel da kuma man jiragen sama, inda kuma ya ce litar mai miliyan 37 suke fatan cimma fara dorawa manyan jiragen ruwa, amma a halin yanzu suna iya lodin litar man miliyan 26. Ko wannan mataki zai kawo karshen shigar da tatatcen mai cikin Najeriya ke nan? Kan haka ne Khamis Saleh ya zanta da Dr Abdullahi Abubakar Gwandu, na kwalejin kimiya da fasaha ta kasa da ke Kaduna.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar zantawar tasu.......

  • Dr Kasim Garba Kurfi kan matakin CBN na kara yawan jarin bankunan kasar

    03/04/2024 Duración: 03min

    Babban Bankin Najeriya ya bai wa bankunan kasuwancin kasar umarnin kara yawan jarin su domin tafiya da zamani, wanda ya kunshi jarin naira biliyan 50 ga bankunan shiya da kuma naira biliyan 500 ga bankunan da ke hada hada da kasashen ketare. Domin sanin tasirin wannan mataki, Abdulkadir Haladu Kiyawa ya tattauna da masanin tattalin arziki, Dr Kasum Garba Kurfi. Ku latsa alamar sauti don jin yadda zantawar su ta gudana.........

  • Comrade Bashir Dauda kan halin tsaro da ake ciki a jihar Katsina

    02/04/2024 Duración: 03min

    Jihar Katsina da ke Najeriya na daya daga cikin jihohin da ke fama da matsalar 'yan bindiga a yankin Arewa maso Yammacin kasar. Duk kokarin hukumomi jihar na sasantawa da 'yan bindigar yaci tura. Dangane da halin da jihar ke ciki kan matsalolin tsaro, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Comrade Bashir Dauda sakataren kungiyar muryar talata a Najeriya.Ku latsa alamar sauti don jin cikakken zantawar tasu.....

  • Reverend Yakubu Ishaku kan bikin ranar Easter

    01/04/2024 Duración: 03min

    A wannan rana ce Kiristoci a fadin duniya ke bikin ranar Easter, don  tunawa da ranar da Yesu Almasihu ya tashi daga matattu. Tun daga Lahadin da ta gabata ake ta addu’o’i domin wannan rana. A kan haka ne Michael Kuduson ya tattauna da Reverend Yakubu Ishaku, na majami’ar First English Baptist Church a jihar Kaduna ta Najeriya. Kulatsa alamar sauti donjin yadda zantarsu ta gudana.......

  • Dr Yahuza Getso kan bukatar Tinubu ta ayyana masu satar mutane a matsayin 'yan ta'adda

    28/03/2024 Duración: 03min

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bukaci ayyana masu garkuwa da mutane a matsayin 'yan ta'adda, matakin da zai bai wa jami'an tsaro damar amfanin da karfin da ya wuce kima wajen kai musu hari. Wannan ya biyo bayan kubutar da daliban makarantar Kuriga sama da 100 da akayi garkuwa da su. Domin sanin tasirin matakin, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da masanin harkar tsaro, Dr Yahuza Getso. Ku latsa alamar sauti don jin yadda zantawar su ta gudana.......

  • Farfesa Jibrin Ibrahim kan zaben Senegal da aka gudanar a karshen mako

    27/03/2024 Duración: 03min

    Bayanai daga Senegal sun tabbatar da Bassirou Faye 'dan shekaru 44 a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi a a karshen mako, wanda zai bai wa matashin damar zama shugaban kasa mafi karancin shekaru a tarihin kasar. Wannan zabe ya dauke hankalin duniya ganin irin matsalolin da aka samu kafin zaben wanda ya kaiga rasa rayuka da kuma yadda mutumin da bai yi fice a siyasar kasar ba ya samu nasara. Dangane da tasirin zaben, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Jibrin Ibrahim na Cibiyar Bunkasa Dimokiiradiya da ya sanya ido akan yadda zaben ya gudana a Dakar,Ku latsa alamar sauti don jin yadda zantawarsu ta gudana.....

  • Aminu Kuriga kan kubutar da daliban da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su

    26/03/2024 Duración: 03min

    A ƙarshen makon da ya gabata ne labarin ceto ‘yan makarantar garin Kuriga ta ƙaramar hukumar Chikun a jihar Kaduna ta Najeriya da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su ya karaɗe kafafen yaɗa labarai da shafukan sadarwar intanet.  Sai dai a yayin da hakan ya tabbata a wannan Litinin, ba a samu miƙa waɗannan yara ga iyayensu kamar yadda gwamnatin jihar Kadunar ta alkwarta ba.Dannan alamar saurare don jin tattaunawar sa da Micheal Kuduson.

  • Hon Muktar Ishaq Yakasai kan sukar da wasu ke wa gwamnatin Tinubu

    25/03/2024 Duración: 03min

    Duk da matakai da mahukunta a Najeriya ke cewa sun dauka domin tunkarar manyan matsalolin da kasar ke fama da su, da suka hada da na tsaro da kuma tsadar rayuwa, toh amma mafi yawan al'ummar kasar cewa suke yi a zahirance babu wani tasiri da wadannan matakai ke yi wajen shawo kan wadannan matsaloli. Toh sai dai Hon Muktar Ishaq Yakasai, daya daga cikin magoya bayan shugaba Bola Ahmed Tinubu, na ganin cewar ya kamata a yi wa shugaban adalci, lura da irin matsalolin da gwamnatinsa ta gada.Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawarsu da Abdoulkarim Ibrahim Shikal.....

  • Mukhtar Bello kan rikicin siyasar Senegal

    22/03/2024 Duración: 03min

    A wannan Juma’a ake kammala yakin neman zaben shugaban Senegal, kasar da rikicin siyasa da ya auku a cikinta a baya-bayan nan ya gaza yin mummunan tasiri a kanta duk kuwa da jan hankalin duniya da lamarin ya yi. Hukumar zaben kasar ta ce kimanin mutane miliyan 7 ne suka yi rajistar kada kuri’a a zaben da ‘yan takara 19 suka raba rana.Masu sharhi da dama sun lura da yadda duk da rikice-rikicen siyasa da suka taso ba a samu wani tashin hankali da ya taka wa shirin zaben birki ba.Kan haka ne Michael Kuduson ya tattauna da Dakta Mukhtar Bello, malami a bangaren  kimiyyar siyasa a jami’ar Bayero da ke Kano a Najeriya.Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.

  • Farfesa Tukur Abdulkadir kan ziyarar da Blinken a yankin Gabas ta Tsakiya

    21/03/2024 Duración: 03min

    Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya sake komawa a Yankin Gabas ta Tsakiya a ci gaba da kokarin da kasashen duniya ke yi don samar da tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas. Daga farkon wannan rikici wanda ya barke a ranar 7 ga watan Oktoban bara zuwa yanzu, sau da dama Amurka na cewa tana yunkuri domin samar da tsagaita wuta a wannan yaki da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane kusan dubu 35 da kuma raba sama da milyan biyu da gidajensu. Farfesa Tukur Abdulkadir malami a jami’ar jimi’ar jihar Kaduna, na ganin cewa, da dagaske Amurka ke yi, da tuni an kawo karshen wannan yaki.Ku latsa alamar sauti don jin zantawarsa da Abdoulkarim Ibrahim Shikal.......

página 1 de 2